Bayan Shawarar Gwamnoni, Majalisa Za Ta Zauna domin Tabbatar da Kudirin Haraji da Gaggawa

Bayan Shawarar Gwamnoni, Majalisa Za Ta Zauna domin Tabbatar da Kudirin Haraji da Gaggawa

  • Majalisar Dokoki ta Kasa za ta dawo zamanta a yau domin hanzarta amincewa da kudirin gyaran haraji, bayan hutun Kirsimeti da aka yi a shekarar da ta gabata
  • Gwamnoni da sarakunan Arewa sun bukaci a janye kudirin harajin, suna masu cewa zai kara talautar da yankin, amma majalisar na shirin ci gaba da tattaunawa
  • Ana sa ran Majalisar Wakilai za ta dakatar da muhawarar har zuwa Laraba, yayin da Majalisar Dattawa ke ci gaba da nazari kan kudirin harajin da aka kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Majalisar Dokoki ta Kasa za ta dawo zama a yau Talata domin hanzarta amincewa da kudirin gyaran haraji.

Bayan zaman farko na 2025 da aka yi a ranar 14 ga Janairu, majalisar ta dage zaman har zuwa 28 ga wata don bada damar kare kasafin kudin 2025 da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga ganawa da ministoci da manyan kusoshin gwamnati a Abuja

Ana hasashen majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji
Bayan bukatar gwamnoni kan kudirin haraji, majalisa za ta yi zama kan lamarin. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Godswill Obot Akpabio.
Asali: Twitter

Kudirin haraji: Gwamnoni na dakon zaman Majalisa

Sai dai daga bisani, an kara dage zaman zuwa ranar 4 ga Fabrairun 2025 domin bai wa kwamitoci isasshen lokaci su kammala tattaunawa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin tafiya hutu na Kirsimeti, kudirin gyaran haraji da Tinubu ya gabatar ya ja hankalin ‘yan majalisa, musamman daga arewa, tare da gwamnonin yankin da sarakuna.

Majiyoyi masu tushe sun tabbatar cewa wasu gwamnonin na bibiyar matakin da majalisar za ta dauka a kan kudirin harajin.

“Sanarwar da gwamnonin suka fitar ita ce matsayinsu, kuma suna fatan samun fahimtar juna daga ‘yan majalisa."

- In ji wata majiya

Majalisar wakilai ta dakatar da zamanta

Majiyoyi daga shugabannin majalisar sun tabbatar cewa kudirin zai samu amincewa cikin gaggawa yayin da majalisar ke komawa yau.

Sai dai an ce Majalisar Wakilai za ta jinkirta muhawarar zuwa gobe Laraba, domin karrama marigayiya, Hon. Adewunmi Onanuga, wanda ya rasu a ranar 15 ga Janairun 2025.

Kara karanta wannan

'Za mu iya': Tinubu ya dauki mataki da Amurka ta janye tallafin yaki da cutar HIV

Wata majiya ta bayyana cewa Majalisar Dattawa, wadda ta riga ta amince da kudirin a karatu na biyu, za ta ci gaba da nazarinsa domin dacewa da matsayar da gwamnonin suka cimma.

A baya, Majalisar Dattawa ta tura kudirin zuwa kwamitinta na harkokin kudi tare da bada wa’adin makwanni shida domin gudanar da sauraron jama’a da komawa majalisa da sakamakon bincike.

A Majalisar Wakilai kuwa, ‘yan majalisa sun dakatar da tattaunawa kan kudirin harajin ba tare da wata wa’adi ba.

An soke muhawarar ne a cikin wata sanarwa bayan ‘yan majalisar Arewa 73 sun nuna adawa.

‘Yan majalisar na fatan amincewa da kudirin cikin gaggawa, tare da sanya wa’adin kammalawa kafin karshen watan Maris, kamar yadda wata majiya ta bayyana.

Tinubu ya magantu kan amfanin kudirin haraji

Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake shaida wa 'yan Najeriya cewa kudirorin gyaran haraji za su taimaki kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Jigawa ta ware wa 'yan majalisa N30bn don yaki da talauci

Bola Tinubu ya bayyana haka ne a wani taro da ya gudana a Ibadan, inda ya ce bai dace a rika samun matsala a kan batun ba.

Shugaban kasar na wannan roko ne a lokacin da Arewa ta kafe a kan kin amincewa da kudirin harajin da aka gabatar gaban majalisa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.