Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Fadi Dalilin Kashe N2.5bn a kan Auren Gata

Gwamnatin Abba Gida Gida Ta Fadi Dalilin Kashe N2.5bn a kan Auren Gata

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa daukar nauyin daura aure ba abu ne da ake yi a Najeriya kawai ba, ana yi a wasu wuraren
  • Daraktan hukumar Hisbah, Abba Sa’idu Sufi, ya ce kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, Iran, da Canada su na irin wannan
  • Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin kashe Naira biliyan 2.5 domin dakile barna da yaduwar zinace-zinace da sun sabawa addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba a Kano ko Najeriya ne kadai ake daukar nauyin daura auren gata ba.

Darakta a hukumar Hisbah ta Kano, Abba Sa’idu Sufi, ya bayyana cewa kasashen da su ka ci gaba su na daukar nauyin irin wannan aure.

Kara karanta wannan

"Su na cewa maulidi bidi'a ne," Sarkin Kano ya yi raddi a kan 'Qur'an convention'

Abba Gida
Hukumar Hisbah ta yi bayanin kashe N2.5bn a kan auren zawarawa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

A wani labari da ya kebanta da jaridar Aminiya, Abba Sufi ya bayyana cewa hatta kasashen da su ka ci gaba kamar Amurka su na irin wanna aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ba ya ga Amurka inda aka dauki auren mutane akalla 700, Iran, Canada da wasu kasashen duniya su na daukar irin wannan aure.

Kano: Akwai matsaloli sakamakon rashin aure

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta kashe N2.5bn ne domin dakile barna da zinace-zinace a tsakanin al'umar jihar.

A kalaman daraktan hukumar Hisbah, Abba Sufi:

"A kasashen Larabawa, ana yinsa. Iraq, inda aka yi yake-yake, su ma sun yi wadannan, inda aka kashe mazaje. An yi kokarin hada mataye a yi masu aure, domin hana yaduwa zinace-zinace a tsakanin al'umma.

Ya bayyana cewa a matsayin Kano na Musulmar jiha, gwamnati ta na sane da kalubalen da ke hana wasu yin aure, musamman matsalolin kayan daki da makamantansu.

Kara karanta wannan

"Gwamnatinmu ba za ta raga ba," Abba Gida Gida ya zare takobin yaki da rashawa

Hisbah ta kare shirin gwamnatin Kano

Hukumar Hisbah a Kano ta bayyana cewa gwamnati ta bayyana cewa gwara a karar da kudin jihar a wajen auren gata da a samu masu saba wa Allah SWT ta hanyar zina.

Daraktan hukumar, Abba Sufi ne ya bayyana haka, inda ya ce Kano ce jiha tilo da ke kokarin dakile wasu daga cikin abubuwan da Mahallici ya haramta ga bayinSa.

"Jihar Kano ce kadai a Najeriya yanzu ake hana sha da fatauci na giya. Ba inda ake haramta shan giya kamar jihar Kano.

Abba Sufi ya na ganin wannan aiki da gwamnati ta dauko zai taimaka wajen sanya albarka a cikin kudinbaitul Malin jama'a.

Su wa za a yi wa auren gata a Kano?

Hukumar Hisbah ya bayyana cewa auren gata da aka gudanar a baya, ya hada da 'yan Kano da wadanda ba 'yan asalin jihar ba, amma ana dakon umarnin na wannan shekara.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kama 'yan 'daɗi soyayya' da suka yi aure a wurin shakatawa a Kano

Darakta a hukumar ya bayyana cewa, amma a wannan lokaci, ana jiran umarni daga gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen sanya Musulmi da wanda ba Musulmi ba da ke zaune a jihar.

Gwamnatin Kano ta ware kudin auren gata

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta amince da za ta fitar da akalla Naira miliyan 854 domin gudanar da auren zawara, inda za a yi amfani da kudin wajen biyan sadaki da kayan daki.

Zababben gwamna, Abba Gida Gida da da aka zaba a karkashin inuwar NNPP ya dauki matakin ne a jim kadan bayan ya karbi ragamar mulki daga gwamna Abdullahi Umar Ganduje na APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.