An Koma Ruwa: Hatsabibin Dan Bindiga da Aka Sako daga Nijar Ya Dawo Katsina
- Jagoran ‘yan bindiga Bammi Yarma ya dawo Najeriya bayan fitowa daga gidan yari a Nijar, bayan zaman kurkuku na shekaru tara
- Bayyanarsa ya jefa fargaba a jihohin Katsina, Zamfara da Sakkwato, ganin yadda yake da tasiri tsakanin shugabannin ‘yan bindiga
- Rahotanni sun ce manyan shugabannin ‘yan bindiga sun ba shi bindigogi masu yawa, wanda hakan na iya ƙara yawan hare-hare
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Kachallah Bammi Yarma, wanda aka tsare a Jamhuriyar Nijar tun 2015, ya fito bayan cika wa’adin daurin shi.
Bammi Yarma, wanda aka fi sani da jagoran shugabannin ‘yan bindiga, ya dawo yankin Arewa maso Yamma, musamman jihar Katsina, bayan shekaru tara.

Asali: Original
Hatsabibin dan bindiga ya fito daga kurkuku
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa an cafke Bammi Yarma a 2015 a lokacin mulkin tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, yayin da yake safarar makamai da raƙuma tara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da aka kama shi, an kwace dabbobi fiye da 1,000 daga hannun ƙungiyarsa, wanda hakan ya katse musu babbar hanyar samun kayayyaki.
An gurfanar da shi kuma aka yanke masa hukunci a Jamhuriyar Nijar, inda ya yi zaman gidan yari na tsawon shekaru tara.
Dan bindigar ya fara jagorantar hare-hare
Rahotanni sun ce Bammi Yarma ya sake bayyana a yankin Arewa maso Yamma, inda ya jagoranci hare-hare da garkuwa da mutane da satar shanu.
Bayyanarsa ya je mutane cikin fargaba, ganin irin tasirin da yake da shi a tsakanin shugabannin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, da Sakkwato.
Rahotanni sun ce wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga suna girmama shi, har suna ba shi makamai masu yawa, ciki har da bindigogi biyar zuwa goma.
Ana fargabar karuwar ta'addanci a Arewacin Najeriya
Masu nazari kan tsaro na ganin bayyanarsa na iya haifar da ƙaruwar hare-hare da tashin hankali a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan
Yayin da ake shirin zaben gwamna, an fadi shirin APC domin kwace mulki cikin sauki
Bammi Yarma ba kawai yana gudanar da ta’addanci ba ne, har ma ya na kashe wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga, ciki har da Kachallah Kundu.
Ana tsoron cewa dawowarsa na iya tayar da sababbin rikice-rikicen ƙungiyoyin ‘yan bindiga ko ƙarfafa hare-haren da ake kai wa al’ummomi.
Sunan Bammi Yarma ya wuce iyakar Najeriya, har wasu ƙungiyoyin ta’addanci a Nijar da yankin Sahel na tsoron tasirinsa.
Katsina: 'Yan bindiga sun farmaki gidan ciyaman
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu ƴan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari a gidan shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi, jihar Katsina.
A yayin wannan mummunan farmakin, ƴan bindigan sun kashe wani jami’in ƴan sanda da ke tsaron gidan shugaban ƙaramar hukumar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng