Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya kaddamar da asusun lamunin kawar da cutar Kanjamau N62bn
- Bayan shekara da shekaru ana yakar Kanjamau a Najeriya, har yanzu da sauran rina a kaba
- Shugaban kasa ya kaddamar da asusun lamunin N62bn don takaita yaduwar cutar a fadin Najeriya
- Manyan attajiran Najeriya ne zasu bada gudunmuwan kudade wajen gudanar da ayyukan asusun
Abuja - A ranar Talata, 1 ga Febrairu, Shugaba Muhammadu Buhari da manyan jami'an gwamnati da attajirai sun dira taron kaddamar da asusun lamunin cutar Kanjamau HIV/AIDS.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnati ba za tayi kasa a gwiwa wajen takaita yaduwar cutar ba.
Shugaban kasan ya jinjinawa hukumar takaita yaduwar cutar HIV, NACA.
Legit ta halarci taron da ya gudana a fadar Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.
A cewarsa:

Kara karanta wannan
An yankewa Hedmasta hukuncin share filin kwallo tsawon wata 3 kan satar kudin makaranta
"Daga yanzu, ina kyautata zaton asusun lamunin HIV zai taimaka wajen cimma manufar kawar da yaduwar Kanjamau nan da shekaru biyar."

Asali: Original
Hukumar NACA ta kafa asusun lamunin ne domin yaki da yawaitar masu kamuwa da cutar HIV a Najeriya.
Mambobin kwamitin dattawan asusun sun hada da shugaban bankin Access, Herbert Wigwe; Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote; Dirakta Manajan Total, Mike Sangster; da Managan kamfanin man Shell, Osaguue Okunbor.
Sauran sune shugaban kamfanin Julius Berger, Lar Richter; Shugaban hukumar NACA, Gambo Aliyu; da tsohon shugaban hukumar NACA, Aliyu.
An nada Jekwu Ozoemene matsayin shugaban kwamitin asusun lamunin.
Asali: Legit.ng