'Yan Kasuwa Sun Sanar da Saukar Farashin Fetur bayan Karyewar Abinci
- Masu sayar da mai sun bayyana cewa farashin litar fetur da ake shigo da shi ya dawo N922.65, ƙasa da na matatar Dangote
- Rage farashin na iya sa masu kasuwancin man fetur su koma shigo da fetur daga ketare saboda samun riba mai yawa
- Masana sun bayyana cewa raguwar farashin na da alaƙa da yanayin kasuwannin duniya da sauye-sauyen musayar kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Masu sayar da man fetur a Najeriya sun bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen shigo da man fetur zuwa ƙasar nan ya ragu zuwa N922.65.
Rahotanni sun nuna cewa saukin farashin ya sanya saukar kudin litar mai kasa da yadda matatar Dangote ke sayarwa a kan N955.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa raguwar farashin ya shafi kuɗin jigilar kaya, harajin shigo da kaya, da kuma tasirin canjin kudin waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana hasashen hakan na nuna yiwuwar masu kasuwancin mai su koma shigo da man fetur daga ƙasashen waje maimakon saye a matatar Dangote.
Farashin shigo da fetur Najeriya ya ragu
Wani babban dan kasuwa wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa an samu saukin farashin shigo da man fetur Najeriya.
Dan kasuwar ya ce:
“Farashin fetur da aka shigo da shi ya fi sauƙi ga masu kasuwanci, don haka ba za ka iya zargin waɗanda suka koma shigo da shi daga ketare ba.”
The Cable ta wallafa cewa raguwar farashin litar fetur da aka shigo da shi zai iya jawo hankalin 'yan kasuwa su koma kan tsarin shigo da kaya daga waje.
Hakan na zuwa ne bayan an bayyana cewa hauhawar farashin man fetur da aka samu a kwanakin baya ya biyo bayan tsadar ɗanyen mai ne a kasuwannin duniya.
Farashin fetur ya sauka a gidajen mai?
Duk da wannan raguwar farashi, litar fetur har yanzu tana kan farashi mai tsada a wasu gidajen man Najeriya, inda manyan dillalai ke sayar da lita tsakanin N990 zuwa N1,010 a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa farashin jigilar kaya da aka ƙiyasta ya dawo N922.65 a ranar Juma’a, wanda ya ragu daga N943.75 da aka sanar a ranar Alhamis.
Gidajen mai da suka rage farashi
Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa wasu gidajen mai sun rage farashin su a wasu jihohin Najeriya.
Gidan man Nipco ya rage farashin daga N965 zuwa N960, yayin da Aiteo ya rage daga N980 zuwa N960.
A daya bagnaren, an ruwaito cewa gidajen man Swift da AA Rano suma sun rage farashin litar mai zuwa N960. A jihohin Delta da Kalaba an cigaba da sayar da litar mai tsakanin N972 zuwa N990.
Fetur da aka shigo sad shi na karshe
Rahotanni sun nuna cewa masu sayar da mai sun shigo da tan 57,301 na fetur tsakanin ranar Talata 21 ga Janairu zuwa Laraba 22 ga Janairu.
An ruwaito cewa hakan na tabbatar da cewa lamarin na nufin lita miliyan 76.84 aka shigo da su a cikin kwanaki biyu kacal.
Wani jami’in masana’antar mai ya ce shigo da fetur ya saba wa yarjejeniyar da aka cimma da Dangote, inda aka ba matatarsa kwanaki 180 domin wadatar da kasar nan da mai.
Duk da haka, kakakin 'yan kasuwar man fetur, Chinedu Ukadike, ya ce yarjejeniyar ba ta hana kowa shigo da fetur daga ketare ba.
NLC ta bukaci rage kudin mai
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan duba sauke farashin mai.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan kwadago sun ce akwai bukatar a tausaya wa 'yan Najeriya a rage farashi domin saukaka musu wahalar rayuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng