Ana Maganar 'Qur'anic Festival', Gwamnati Ta Fito da Shiri ga Almajiran Najeriya
- Hukumar Almajirai ta sanar da shiri domin bayar da horo na musamman na wata tara ga almajirai masu karatu a tsangaya
- Rahotanni sun nuna cewa za a koyar da sana’o’in dogaro da kai ga mahaddatan Alkur’ani domin su samu damar dogaro da kai
- A bayanin da hukumar ta yi, almajiran da suka cika sharuddan da aka gindaya za su iya shiga shirin daga yau zuwa 30 ga Janairu, 2025
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Hukumar Ilimin Almajirai da Yaran da Ba sa Zuwa Makaranta, karkashin jagorancin Dr Muhammad Sani Idris, ta sanar da shirin horar da daliban tsangaya.
Shirin, wanda aka tsara tsawon watanni tara, zai bai wa almajiran tsangaya damar samun ilimi da sana’o’i, wanda zai basu damar dogaro da kansu a rayuwa.

Asali: Getty Images
Sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook ya nuna cewa shirin zai fara ne kafin 15 ga watan Fabrairu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sharuddan shiga shirin almajirai
A cewar sanarwar, akwai wasu sharudda da dole almajiran tsangaya su cika kafin samun gurbi a wannan shirin. Sharuddan sun hada da:
1. Mai neman shiga dole ya zama dalibin tsangaya kuma mahaddacin Alkur’ani
2. Shekarunsa ya kasance tsakanin 16 zuwa 26.
3. Ya kasance yana da cikakkiyar lafiya domin karbar horo daga karfe 8 na safe zuwa 6 na yamma
4. Dole ya samu amincewar malaminsa da kuma iyayensa
5. Ka da ya kasance yana da wata matsala da jami’an tsaro ko kotu
Sanarwar ta kuma jaddada cewa guraben karatun ba su da yawa, don haka sai wanda ya cika sharuddan ake maraba da shi.
Makasudin shirin horas da almajirai
Dr Muhammad Sani Idris ya bayyana cewa an shirya shirin ne domin ilmantar da daliban tsangaya da kuma koya musu sana’o’in dogaro da kai.
A cewarsa, manufar wannan horo ita ce taimakawa almajirai su zama mutane masu cin gashin kansu ba tare da sun dogara da wani ba wajen samun abin rayuwa.
Yadda almajirai za su yi rajista
Hukumar ta bayyana cewa duk mai sha’awar shiga wannan shirin zai iya tura sunansa, sunan tsangayarsa, garinsa, da sunan malaminsa ta shafinta na Facebook.
Haka zalika, za a iya aiko da bayanai ta lambar 09064313510 ko ta WhatsApp tare da nuna cewa mutum yana sha’awar shiga shirin.
Amma, wajibi ne a tabbatar da cewa an aika bayanan kafin ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, 2025, wanda ya yi daidai da 30 ga watan Rajab, 1446.
Ana ganin cewa shirin horar da almajirai a jihar Kaduna zai zama wata hanya ta kawo sauyi a rayuwar daliban tsangaya a Najeriya.
Farfesa a jami'ar Legas ya haddace Kur'ani
A wani rahoton, kun ji cewa wani farfesa a jami'ar Legas mai suna Tajudden Yusuf ya yi zarra wajen haddace Al-Kur'ani mai girma bayan daukar tsawon shekaru.
Rahoton Legit ya nuna cewa Farfesan ya shafe shekaru 59 a rayuwarsa kafin haddar kuma ya yi kira ga al'umma kan karatun Kur'ani.
Asali: Legit.ng