"Danyen Mai Ya Tashi a Duniya," Dangote Ya Fadi Saukin da Ya Yi a Karin Farashin Fetur
- Matatar Dangote ta ce ta yi karin 5% kacal daga N899.50 zuwa N950 ga kowace litar fetur idan aka kwatanta da tsadarsa a duniya
- Matatar ta ce farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya karu da 15%, wanda ke nuna cewa an yi wa 'yan Najeriya sauki
- Dangote ya dauki nauyin karin kudin jigilar man don tabbatar da cewa an sayar da fetur a farashin bai ɗaya fadin Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa ta yi karin farashin fetur ga 'yan kasuwa ne sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Anthony Chiejina, babban jami’in sadarwa da dabarun kasuwanci na rukunin kamfanin Dangote, ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ya na cewa danyen mai shi ne babban kayan sarrafa man fetur, don haka duk wani tashin farashi a kasuwannin duniya yana tasiri kai tsaye kan farashin man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 17 ga Janairu, matatar Dangote ta sanar da kwastomominta ta hanyar sakon imel cewa farashin fetur a tashar lodinta ya karu zuwa N955 kowace lita.
Matatar Dangote ta bayyana sabon farashin fetur
Jaridar The Cable ta wallafa cewa matatar ta ce ta na da cikakken fahimtar muhimmancin fetur mai saukin farashi ga ‘yan Najeriya, kuma tana kokarin samar da shi da sauki.
Sanarwar da Anthony Chiejina ya fitar ta ce;
“Mun yi karin 5% kacal daga N899.50 zuwa N950 kowace lita. Wannan karin bai yi yawa ba idan aka kwatanta da tashin 15% na farashin danyen mai a kasuwar duniya, wanda ya kai daga $70 zuwa $82 cikin kwanaki kaɗan, tare da kari na kimanin $3 a kan kowace gangar danyen mai na Najeriya."
Dangote na kokarin a sayar da fetur da sauki
Matatar ta bayyana cewa duk abokan huldarta, ciki har da Ardova, Heyden, da MRS Holdings, za su sayar da man fetur ga ‘yan Najeriya a farashin N970 kowace lita a fadin ƙasar.
Sanarwar ta ce;
“Mun dauki nauyin karin kudin jigilar man don tabbatar da cewa farashin ya kasance daya a jihohi 36 da Abuja. Mun kuma dauke kimanin 50% na karin farashin da kasuwar mai ta duniya ta fuskanta."
Dalilin Dangote na kara farashin da sauki
Anthony Chiejina ya ce da matatar ba ta dauke wani nauyi ba, za a rika sayar da fetur ne a kan farashin N1,150 da N1,200 kowace lita, maimakon N970 da ake sayarwa a halin yanzu.
Ya ce an yi haka ne domin taimakon ƴan ƙasa, tare da bayyana godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu kan bullo da shirin sayar da danyen mai da Naira gare matatar Dangote.
Dangote: Sanata Sani ya soki karin farashin fetur
A baya, kun ji cewa tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya nuna rashin jin daɗinsa kan ƙarin farashin man fetur da Matatar Dangote ta aiwatar kwanan nan.
Shehu Sani ya bayyana cewa 'Yan Najeriya sun yi fatan matatar Dangote za ta rage farashin man fetur don saukaka wa jama'a, wannan ta sa karin farashin bai masa dadi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng