Wani mutum ya mutu bayan ya kwana da karuwa a otel (Bidiyo)

Wani mutum ya mutu bayan ya kwana da karuwa a otel (Bidiyo)

Wani mutum mai matsakaicin shekaru da ba a bayyana sunansa ba ya mutu bayan ya kwana da wata karuwa a otel.

Wasu da mutanen da suka shaida afkuwan lamarin sun tsinci maganin karfin maza a dakin wadda hakan yasa suke tsamanin mutumin ya mutu ne bayan ya sha magungunan kara karfin mazan.

A yayin da ta ke bayar da bayyani a kan abinda ya faru, karuwar da ta ce sunan ta Precious daga jihar Akwa Ibom ta ce abokin marigayin ne ya gayyace ta zuwa otel din domin ta kwana da abokinsa.

Precious ta bayyana cewa mutumin ya yi ta sharbar barcinsa cikin dare duk da cewa ba ta gan shi yana shan magungunan ba. Ta ce ya kwanta da ita misalin karfe 5 na asuba sannan ya koma barcinsa.

Wani mutum ya mutu bayan ya kwana da karuwa a otel
Wani mutum ya mutu bayan ya kwana da karuwa a otel
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matar aure ta lakada wa mijin ta duka domin ya gasa yi mata ciki

A lokacin da ta tashi za ta tafi ne sai Precious ta lura cewa bai tashi daga barcin ba kuma tana son ta karba kudin ta.

Da farko tana zargin kaman baya son biyan ta kudinta ne amma sai ta lura baya motsi bayan ta mangare shi. Karuwar ta ce a lokacin ne ta razana ta fita waje ta nemi a zo a taimaka mata.

Ga dai bidiyon bayyanin da ta yi wanda tuni ya karade dandalin sada zumunta da shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel