"Ya Sha Maganin Kara Karfin Maza": Matashi Ya Mutu Yana Tsaka Da Kwasar Gara Wajen Abokiyar Sharholiyarsa

"Ya Sha Maganin Kara Karfin Maza": Matashi Ya Mutu Yana Tsaka Da Kwasar Gara Wajen Abokiyar Sharholiyarsa

  • Matashi ya ce ga garinku yayin da yake tsaka da nuna kurewarsa yayin kwanciya da wata abokiyar sharholiyarsa
  • Budurwar tasa da makwabta suka lokacin da ya shiga da ita daki ta tsere bayan ganin halin da ake ciki
  • Bincike ya nuna maganin kara karfin maza ya sha domin an gano sauransa a cikin dakinsa da wasu lemukan kara kuzari

Rivers - Wani mai aski wanda aka ambata da suna Otubong ya mutu bayan zargin kwanciya da abokiyar sharholiyarsa a yankin Mile 2 da ke Port Harcourt, jihar Ribas, a ranar Juma’a.

Jaridar Punch ta rahoto cewa an ga mutumin a yammacin ranar Alhamis yana shiga daki da budurwar a yankin da ke da cunkoson jama’a.

Tsawirar jihar Ribas
"Ya Sha Maganin Kara Karfin Maza": Matashi Ya Mutu Yana Tsaka Da Kwasar Gara Wajen Abokiyar Sharholiyarsa Hoto: The Sun
Asali: UGC

An kuma tattaro cewa mutumin mai matsakaicin shekaru ya sha wasu magungunan kara kuzarin maza, ciki harda wani barasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Ta Bada Umarni a Ruguza Gidaje, Rigima Ta Kaure da ‘Yan Unguwa

Sai dai kuma, a safiyar ranar Juma’a, daya daga cikin makwabtansa da ya shiga duba shi ya tarar da kofarsa a bude.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makwabcin ya ce:

“Da safen nan (Juma’a) ne daya daga cikin makwabtansa ya je karbar abu a gidansa sai ya ga cewa kofar a bude take.
“Ya ce bayan ya kwankwasa tare da kiran sunansa ba tare da an amsa masa ba sai kawai ya yanke shawarar shiga ya ga mutumin.
“Don haka sai ya fasa ihu sannan nan take ya fito ya sanar da sauran mazauna yankin abun da ya gani. Sai mutane suka fito, suka dauke shi sannan suka kai rahoton lamarin wajen yan sanda."

Maganin kara karfin maza ya sha, Majiya

A halin da ake ciki, wata majiya ta yan sanda ta sanar da manema labarai cewa an gano lemun kara kuzari biyu, fakitin tramadol biyu da wani maganin kara karfin maza a dakinsa, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Muhammadu Sanusi II Ya Fayyace Dalilan Zuwa Aso Rock da Abin da Ya Fadawa Tinubu

Lamarin ya ja hankalin mazauna unguwannin da ke kusa, wadanda suka je tabbatar da abun da suka ji kafin a kai rahoton lamarin ofishin yan sanda na Azikiwe a Port Harcourt.

Martanin yan sanda

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ba domin bata amsa kiran wayar da aka yi mata ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Dan Najeriya ya hana fasinjoji sauka daga jirgin sama saboda batan kilishinsa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan Najeriya ya haddasa yar dirama inda ya hana fasinjojin jirgin sama sauka bayan sun isa filin jirgin da za su sauka.

Mutumin dai ya nemi jakar da ya yi guzirin kilishi ya rasa lamarin da ya fusata shi har ya kai ga neman kowa ya binciki kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel