Hamshakin Mai Kudin Duniya, Bill Gates Ya Fadi Babban Kuskuren da Ya Yi a rayuwa

Hamshakin Mai Kudin Duniya, Bill Gates Ya Fadi Babban Kuskuren da Ya Yi a rayuwa

  • Hamshakin mai kudin duniya, mamallakin Microsofyt, Bill Gates ya bayyana sakin Melinda French a matsayin babban kuskure
  • Bill Gates ya ce Melinda ta taimaka masa ya samu cimma kololuwar nasara kuma ita ce ta rika kula da mafi yawan ayyukan gida
  • Rabuwa auren ta taba rayuwar Bill sosai, amma ya ce yanzu yana samun farin ciki kuma suna haɗuwa da Melinda lokaci zuwa lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

London - Bill Gates ya bayyana sakin da ya yiwa tsohuwar matarsa, Melinda French Gates, a shekarar 2021 a matsayin "kuskure mafi girma a rayuwarsa."

A wata hira da aka wallafa ranar Asabar, 25 ga Janairu, tsohon shugaban Microsoft ɗin mai shekaru 69 ya bayyana burinsa na samun aure mai dorewa irin na iyayensa.

Kara karanta wannan

Bayan kiran El Rufa'i, Peter Obi ya ce ya yarda da hadakar 'yan adawa a 2027

Bill Gates ya yi magana bayan shekaru da rabuwa da matarsa Melinda French
Bill Gates ya fadi kuskuren da ya tafka da ya rabu da matarsa Melinda French. Hoto: @melindagates
Asali: Twitter

Bill Gates ya tuno rayuwarsa da Melinda

Jaridar The Times of London wadda ta wallafa hirar, kuma manyan kafofin watsa labarai suka wallafa ciki har da jaridar Daily Mail, ta ruwaito Bill Gates yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na yi ƙoƙari in sa Melinda ta zama mai natsuwa fiye da mahaifiyata, amma dukkamu muna da kwadayin samun nasara a rayuwa."

Ya ce ya fi iyayensa ɗaukar lokaci tare da yara, amma Melinda ce ke gudanar da mafi yawan ayyukan gida yana mai cewa "mun yi rayuwa mai daɗi sosai."

Bill Gates ya tuno radadin rabuwa da Melinda

Bill ya yi imanin cewa akwai "wani abin ban sha'awa a gudanar da rayuwar samartaka tare da mutum ɗaya," musamman idan ka samu rabo a tsakani.

"Lokacin da ni da Melinda muka hadu, ina da 'yar nasara ta amma ban shahara cancan ba - amma babbar nasarar ta same ni ne a lokacin da muke tare.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

"Don haka, ta kasance tare da ni a lokacin dadi da wahala. Lokacin da muka rabu, na shiga mawuyacin hali. Lamura sun dagule da ta yi murabus daga gidauniyarmu, na ji ba dadin tafiyarta."

- Bill Gates.

Haduwar Bill Gates a 1987 da rabuwarsu

Gates da Melinda sun fara haɗuwa a 1987 lokacin da Melinda ta zama manajan samfur a Microsoft, kuma suka yi aure a Hawaii a 1994.

A 2000, suka kafa gidauniyar Bill & Melinda Gates domin yaƙi da talauci da cututtuka a duniya, amma Melinda ta yi murabus a 2024, inji rahoton jaridar People.

Lokacin da aka tambaye shi ko saki shine kuskurensa kawai, Bill Gates ya ce:

"Za ka sanya wannan a saman jerin. Akwai sauran kuskuren amma ba su da mahimmanci, wannan shi ne mafi kuskuren da na yi a rayuwa ta.
"Mun shafe shekaru biyu muna fama da damuwa bayan rabuwarmu, amma yanzu bayan kusan shekaru huɗu ina samun farin ciki."

Kara karanta wannan

Su waye ke daukar nauyin ta'addanci? Hafsan tsaro ya fayyace gaskiya kan lamarin

Bill Gates ya zuga Tinubu ya kara haraji

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mai kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya bayyana cewa kudin harajin da ake karɓa a Najeriya bai isa ba, kuma hakan ba zai haɓaka cigaban ƙasa ba.

Furucin hamshakin mai kudin Bill Gates ya yi daidai da lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ke shirin ƙara harajin VAT daga kashi 7.5% zuwa 10%.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.