Fadar Shugaban Kasa Ta Fadi Yadda Aka Zuba Jarin $6.7bn a Bangaren Makamashi
- Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa an samu zuba hannun jari a bangaren makamashi a shekarar 2024
- Hadimar shugaba Bola Tinubu,Olu Verheijen ce ta bayyana hakan ta cikin rahoton da ofishinta ya fitar ranar Laraba
- Ta ce Najeriya ta sanya burin da ta ke son cimma wa wajen samun karin zuba hannun jari a sashen kafin 2029
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan makamashi, Olu Verheijen ta ce an zuba jarin dala biliyan 6.7 a fannin makamashin Najeriya a shekarar 2024. A wani rahoto mai taken ‘Presidency Energy Sector Wrap-Up 2024,’ wanda ofishinta ya fitar a ranar Laraba, bangaren mai da iskar gas ya lakume Dala biliyan 5.5 na na jarin.

Asali: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnati ta kashe Dala miliyan 400 a shirin shugaban kasa na inganta makamashi, Dala miliyan 700 ta tafi domin tsabtace sufuri da kuma makamashin girki.
A cewar mai ba da shawara na musamman, an samu masu zuba jari sun zuba $5.5bn wajen mallakar kadarori, kamar kamfanin Renaissance Consortium da ya saye kamfanin Shell a kan $1.3bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu karin hada-hada a sashen makamashi
Olu Verheijen ta ce kamfanin Seplat Energy Plc a kammala saye Mobil Producing Nigeria Unlimited MPNU daga ExxonMobil Corporation a kan $1.3bn.
Rahoton da ta fitar ya ce;
“Chappal Energies ya kammala siyan Equinor Nigeria Energy Company (ENEC), reshen kamfanin Equinor ASA na Norway a kan $1.2bn.
“Oando Plc ya kammala sayan Kamfanin Mai na Najeriya Agip Oil Company (NAOC) a kan $800m."
An samu zuba jari a bangaren makashin
Rahoton ya bayyana muhimman zuba jarin da aka samu a bangaren mai da iskar gas ta hanyar rangwamen haraji ga wani nau'i na gas da ake shigo wa da shi ta teku.

Kara karanta wannan
"A bar mu da talaucinmu": Shettima ya fadi matsayarsa kan dogara da tallafin turawa
SNEPCO ya zuba jarin $5bn a aikin Bonga North Deep Offshore Project, irinsa na farko a cikin shekaru 10 da zai samar da ganga kusan 110,000 na mai a kowace rana.
Kamfanin Total Energies and Nigerian National Petroleum Company (NNPC) Limited ya zuba jarin dala miliyan 550 a aikin iskar gas na Ubeta.
Makamashi: Gwamnati saita burinta na 2029
Verheijen ta ce Najeriya a yanzu tana kan hanyar samun jarin iskar gas da $5bn nan da shekarar 2029, ta yadda za a kara samar da iskar gas zuwa kasashen waje. Ta kuma ce Najeriya na da damar samun dala biliyan 30 a cikin zurfafa zuba jari a teku nan da shekarar 2029. Ta ce an yi kokarin samun ci gaban tattalin arziki da kuma kara yawan albarkatun makamashin Najeriya.
Ana son a kori Ministan makamashi
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta shawarci Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da ya yi murabus daga mukamin da aka naɗa shi.
Kungiyar ta ce ta ga bukatar haka ne ganin yadda ake ci gaba da samun lalacewar turakun wutar lantarki, da sauran matsaloli a bangaren wadata kasa da hasken wuta.
Asali: Legit.ng