Badakalar $6bn: Gwamnatin Tinubu Ta Tilastawa Buhari ba da Shaida a Kotu? An Gano Gaskiya

Badakalar $6bn: Gwamnatin Tinubu Ta Tilastawa Buhari ba da Shaida a Kotu? An Gano Gaskiya

  • An yaɗa wasu rahotanni masu iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Bola Tinubu ta tilastawa Muhammadu Buhari ba da shaida a gaban kotu
  • Fadar shugaban ƙasa ta fito ta musanta rahotannin tilastawa tsohon shugaban ƙasan ba da shaida a gaban kotun Paris kan kwangilar Mambilla
  • Ta bayyana cewa dukkanin masu ba da shaida domin kare Najeriya a shari'ar, suna yi ne a ƙashin kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan rahotannin da ke yawo cewa ta tilasta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ba da shaida a birnin Paris.

Fadar shugaban ƙasa a daren ranar Asabar, 18 ga watan Janairun 2025, ta musanta batun tilastawa Buhari ko wani ɗan Najeriya ya bayyana a gaban wata kotu a Paris don bada shaida kan shari’ar sasanta rikici.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta samu kudi sama da Naira biliyan 2 daga ɗaura aure a 2024

Fadar shugaban kasa ta musanta tilastawa Buhari
Fadar shugaban kasa ta musanta tilastawa Muhammadu Buhari ba da shaida a Paris Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a shafinsa na X a daren ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daren Asabar, wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo ta wallafa rahoton cewa an kira Buhari a gaban wata kotu a Paris don ya bada shaida kan rikicin kwangilar samar da wutar lantarki na Mambilla wacce ta kai darajar $6bn.

Me gwamnatin Tinubu ta ce kan tilastawa Buhari?

A cikin sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar, ya ƙaryata rahoton cewa an tilastawa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zuwa Paris don ba da shaida kan shari'ar.

Sai dai, hadimin shugaban ƙasan bai musanta cewa akwai wannan shari’ar ba.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa dukkanin ƴan Najeriyar da ke shirin kare Najeriya a shari'ar, suna yin hakan ne a ƙashin kansu da kuma kishin da suke yi wa ƙasar nan.

Kara karanta wannan

"Gidaje 3 na mallaka": Buhari ya fadi inda yake samun kudi bayan sauka daga mulki

"Fadar shugaban ƙasa ta lura da wasu labaran ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta game da wata shari’ar sasanta rikici da ake gudanarwa a Paris, wacce gwamnatin Najeriya ke da hannu a ciki."
“Shari’ar da ake gudanarwa a cikin sirri, wacce bai kamata a wallafa a kafafen watsa labarai ba, ana yinta ne a sirrance har zuwa lokacin da alƙalai na ƙasa da ƙasa za su yanke hukunci."
"Yayin da muke mutunta sirrin shari’ar, muna so mu bayyana ƙarara cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bai tilastawa kowa ba da shaida ko ƙin ba da shaida kan Najeriya ba."
“Dukkan manyan mutanen Najeriya da ke cikin shirin kare martabar ƙasar suna yin hakan ne bisa son ransu da kishin ƙasa. Shugaba Tinubu da ɗaukacin al’ummar ƙasar suna godiya gare su."

- Bayo Onanuga

Ahmed Lawan ya ziyarci Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura cikin jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Buhari, Radda da manyan 'yan siyasa sun yi taron neman nasara ga APC

Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi ƙasar nan tare da tsohon shugaban ƙasan.

Ya kuma nuna godiyarsa kan irin tarbar da ya samu daga wajen Buhari a yayin ziyarar da ya kai masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng