Fitaccen Lauya a Kano Ya Yi Mamakin Kalaman Sarki Sanusi a kan Gwamnatin Tinubu

Fitaccen Lauya a Kano Ya Yi Mamakin Kalaman Sarki Sanusi a kan Gwamnatin Tinubu

  • Fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima ya yi mamakin dalilin Sarkin Kano na kin taimakawa gwamnatin Bola Tinubu
  • A makon da ake ciki ne, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ce ya na hanyar warware matsalolin tattalin arzikin Najeriya
  • Amma Sarki ba zai taimaka da komai ba saboda zargin da ya yi na cewa abokansa da ke gwamnatin ba shi dauke shi aboki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Fitaccen lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam a Kano, Barista Abba Hikima ya yi mamakin kalaman Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II. A wani taro da ya gudana a jihar Legas ne Sarki Sanusi II ya bayyana dalilin da ya sa ba zai ba gwamnatin tarayya shawarwarin tattalin arziki ba.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

Sarki
Abba Hikima ya yi tsokaci a kan kalaman Sarkin Kano Hoto: Abba Hikima/Sanusi II Dynasty
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abba Hikima ya nuna cewa rashin ba da shawarwarin ba halayyar Sarki Muhammadu Sanusi ba ce. Sarkin dai ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta na tafka kura-kurai a manufofin tattalin arzikinta, amma ba zai ce uffan ba saboda ba su 'dauke shi abokin ba.'

Abba Hikima ya yi mamakin kalaman Sarki Sanusi

Barista Abba Hikima ya ce Sarki Muhammadu Sanusi II ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya ta bar jama'ar kasa a cikin kunci saboda tsare-tsarenta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ce Sarkin ya ba da tabbacin dukkanin matsalolin da ake ciki a yanzu, abubuwa ne da za a iya kauce masu don saukaka wa talakawan Najeriya.

Barista Abba Hikima ya shawarci Sanusi II

Lauya mai fafutukar kare hakkin bil'adama, Abba Hikima ya ce bai ga dalilin da zai sa Sarki Muhammadu Sanusi II ya rufe idanunsa ga kura-kuran gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

Ya ce bai fahimci yadda Sarkin zai dauki matakin rufe bakinsa ba duk da cewa ya san gwamnatin tarayya ba ta da kwararrun da za su ba da shawarar tattalin arziki yadda ya dace.

Abba Hikima ya kara da cewa;

To, Sarkin Sanusi, wanda yake da tabbaci cewa matsalolin tattalin arzikin Najeriya na yanzu abu ne da aka hango su kuma za a iya guje masu, kuma ya gane cewa gwamnatin tarayya ba ta da kwararrun masana da za su kawo hanyoyin warware matsalolin tattalin arziki da za su saukaka wa ‘yan Najeriya, ya zabi ya watsar da nauyin da ke kansa na bayyana ra’ayinsa kawai saboda gwamnatin tarayya ta daina zama abota da shi?

Sarki Sanusi ya ƙi taimakawa gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Sarkin Kano 16, Malam Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na yin kura-kurai a tsarin tattalin arzikinta.

Kara karanta wannan

Abin da Kashim Shettima ya ce kan bikin Maulidi a Kano duk da zargin kokarin hana taron

Sarkin ya ce ya na da mafita a kan matsalolin da ake ciki a halin yanzu, amma ba zai taimaka ba saboda abokansa da ke cikin gwamnatin ba su dauke shi a matsayin aboki ba.

Kalaman Sarkin ba za su rasa nasaba da zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na goyon bayan Aminu Ado Bayero a matsayin halastaccen Sarkin Kano ba a yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.