Bayan Fafutukar Dakile Auren Jinsi, Kungiya na Neman Gwamnati Ta Halasta Shi
- Ba a dade da fafutukar dakile yunkurin tabbatar da barin masu son auren jinsi su wala a kasar nan ba, wata kungiya ta bullo da sabon batu
- Kungiyar ta Creative Africa Initiative ta rubuta wasika da tambarin ma'aikatar ilimi ta na neman a bayar da damar tattauna batun auren jinsi
- Tuni gwamnatin tarayya ta barranta kanta da wannan lamari, inda ta ce ya saba da addini, al'ada da ra'ayin akasarin 'yan kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana bacin ranta karara a kan yadda wata kungiya ta Creative Africa Initiative ke fafutukar tabbatar da auren jinsi.
Kungiyar ta kuma kwaikwayi tambarin ma'aikatar ilimi ta kasa, inda ta rubuta wasikar da ke neman a ba wa jama'a dama su tattauna yadda za a halasta haram.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ma'aikatar ilimi ta fitar da sanarwa, inda ta yi tir da wasikar tare da barranta kanta daga abin da kungiyar ta nema.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"DSS ta binciki rajin auren jinsi" - Ma'aikata
Babban sakataren Ma'aikatar ilimi na kasa, Dr. Nasir Auwal Gwarzo ya bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gaggauta binciken wata kungiyar Afrika.
Dr. Gwarzo ya bayyana cewa sun samu rahoton yadda kungiyar ke neman gwamnati ta halasta abin da ya saba da addini, al'ada da yanayin rayuwar 'yan kasa.
Babban sakataren ya ce bukatar kungiyar na bayar da damar tattaunawa a kan amincewa da auren jinsi zai iya jawo tashin hankali a fadin kasar nan, The Cable ta wallafa labarin.
An fallasa yunkurin shigo da auren jinsi
A wani labarin kun ji cewa wasu Farfesoshi a kasar nan sun tona asirin yadda aka dukunkune ra'ayin auren jinsi da neman cusa su a zukatan daliban Najeriya.
Farfesa Salisu Shehu da Farfesa M. B Uthman ne su ka yi fallasar a wata lacca da aka gabatar a ITN, Zariya inda su ka fadi yadda turawa ke shigo da akidar kasashe irinsu Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng