Farfesa Ya Fallasa Dabarar Turawa Wajen Shigowa Najeriya da Akidun LGBTQ a Boye
- Akwai dabaru da ake bi domin tallata manufofin LGBTQ a Najeriya da mutane da yawa ba su Ankara da su ba
- Farfesa Salisu Shehu ya yi wannan bayani ne a wajen wata lacca ta musamman da suka gabatar a ITN Zariya
- Shi ma Farfesa M. B Uthman ya tabo batun yadda kasashen yamma su ke kawo wannan akida a irinsu Najeriya
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kaduna - Masallacin ITN da ke karkashin wannan cibiya ta raya addinin musulunci a garin Zariya ta shirya wata lacca a kan LGBTQ.
A watan da ya gabata, aka gabatar da lacca ta musamman game da manufofin LGBTQ da yadda ake shigo da wannan akidar Najeriya.
ITN ta shirya lacca a kan LGBTQ
Kwamitin wa’azi na masallacin ya gayyato Farfesa Salisu Shehu da Farfesa M. B Uthman su yi magana saboda ce-ce-ku-ce da ake yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ga bukatar hakan ne bayan Najeriya ta shiga yarjejeniyar Samoa wanda aka rika zargin cewa ya na kunshe da zancen auren jinsi.
Legit Hausa ta saurari laccar da Farfesa Ahmad Dogarawa ya jagoranta, mun bibiyi karatun ne a shafin masallacin a kafar Facebook.
Farfesa Shehu ya tona dabarun LGBTQ
Farfesa Salisu Shehu wanda shi ne shugaban jami’ar Al Istiqamah da ke Sumaila a Kano, ya yi bayani a kan yadda ake cuso ra’ayoyin.
Malamin na zamani da musulunci yake cewa ana barbarar irin wadannan tunani na alakar jinsi har a cikin littattafan makarantun boko.
Littatafan da aka kawo manufofin LGBTQ
Daga ciki akwai Basic science & technology – W. K Hamzah, Basic science for JSS ta Madaba’ar Razaq da Active basic science – Tola, dsr
Akwai Cry for justice na Adebola Adefala, New course of English na Eyisi dsr, da wani littafi ‘Stigma’ sai littafin nan na Queen Primer.
LGBTQ: Tasirin wayoyi, wasanni & finanai
Wayoyin zamani da ake yayi a duniyar yau su na cikin hanyoyin dasa wannan akida da ta sabawa addinai da tsarin mulkin Najeriya.
Haka zalika ana amfani da fina-finai da wasannin ‘cartoon’ wajen nuna alakar namiji da namiji, mace da mace, daudu da dai sauransu.
Sannan kasashen turawa su na tallata LGBTQ ta hanyar taurarin da ake koyi da su a duniya.
Salisu Shehu ya ba da shawarar cewa ya kamata malaman cikin gida su rika rubuta littattafan da za a koyawa kananan yara karatu.
Akwai abin tambaya kan bashin kasashen waje
A bayanin da ya yi, M. B Uthman wanda Farfesa ne a bangaren ilmin shari’a, ya bayyana irin boyayyun manufofin kasashen yamma.
Farfesan na jami’ar Ahmadu Bello yake cewa zai yi wahala turawa su ba gwamnati bashin kudi ba tare da wasu ka’idoji da sharuda ba.
Ku na da labari cewa Malam Aminu Abdullahi Chubado yana so ya nemi tallafin jari, amma gwamnati ta cusa ruwa a cikin tsarin NYIF.
Wasu su na ganin tun da musulmi da musulmi su ke kan mulki, ya kamata a fito da tsare-tsaren musulunci, sai dai ba haka abin yake.
Asali: Legit.ng