Rashin Tsaro: Gwamnatin Ta Bullo da Dabarun Fasaha Wajen Yakar Miyagu

Rashin Tsaro: Gwamnatin Ta Bullo da Dabarun Fasaha Wajen Yakar Miyagu

  • Yayin da rashin tsaro ke kara ta'azzara a kasar nan, gwamnatin tarayya ta bijiro da matakan zamani domin yakar mummunar ta'adar
  • Gwamnati ta bayyana cewa an samar da wata manhaja da za ta ba wa 'yan kasa damar tura sakon ta'addancin da ke aukuwa a yankinsu
  • Manhajar da kowa zai iya dorawa a kan wayarsa za ta mika bayanan abubuwan da ke wakana ba tare da bata lokaci ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da wata manhaja da za ta ba wa yan kasa damar mika sakon ta'addanci ko rashin tsaro a yankunansu.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun tsare babbar hanya a Zamfara, an kwashe dimbin matafiya

Gwamnati ta bayyana cewa manhajar da aka yi wa lakabi da mobilizer za ta taimakawa jami'an tsaro wajen samun bayanai tare da daukar matakan dakile ta'addanci.

Teera Konakan
Gwamnati ta bijiro da manhajar mika bayanan ta'addanci kai tsaye Teera Konakan/NurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'an tsaron da za su rika samun bayanan da aka wallafa a manhajar sun hada da 'yan sanda, sojoji, yan sanda da sauran jami'an tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran bayar da bayanan a lokacin da ake ta'addanci zai taimakawa jami'an tsaro wajen dakile harin cikin gaggawa.

Za a wayar da 'yan kasa kan tsaro

Hukumar wayar da kan yan kasa (NOA) ta ce za a dauki gabarar wayar da kan yan Najeriya kan sabuwar manhajar mobilizer.

Darakta janar a NOA, Issa Lanre-Onilu ne ya bayyana haka yayin taron kaddamar da manhajar a babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Daraktan ya roki 'yan jarida su tallafa masu wajen shaidawa mutanen kasar nan muhimmancin amfani da manhajar wurin aika sakon kar ta kwana a kan ta'addanci.

Kara karanta wannan

"Ko mutum 1 ba a kashe a lokacin zanga zanga ba," Inji rundunar 'yan sandan Kano

Ana dakile matsalar rashin tsaro a Borno

A baya mun ruwaito cewa rundunar sojojin kasar nan ta karbi tubabbun 'yan Boko Haram a Kamaru, tare da bayyana adadin wadanda su ka mika wuya.

Shugaban yada labarai na rundunar hadin gwiwa na MJTF, Abdullahi Abubakar ya jaddada cewa dukkanin tubabbun yan Boko Haram ɗin yan Najeriya ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.