Ana Shari’ar Masarautun Kano, Dubban Kanawa Sun Tarbi Aminu Ado a Bidiyo

Ana Shari’ar Masarautun Kano, Dubban Kanawa Sun Tarbi Aminu Ado a Bidiyo

  • Yayin da ake tsaka da shari’ar masarautu a kotu, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga Kanawa bayan sallar Juma’a
  • Aminu Ado ya gudanar da sallar Juma’a a yau a masallacinsa da ke fadar Nasarawa kamar yadda ya yi a makon jiya bayan tube shi daga karaga
  • Aminu Ado ya samu tarba daga dubban masoya wadanda suka yi dandazo domin nuna masa goyon bayan duk da umarnin kotu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya sake gudanar da sallar Juma’a a yau 7 ga watan Yuni a jihar.

Dubban jama’a ne suka tarbi sarkin yayin da ya ke dawowa daga masallacin Juma’a duk da shari’ar da ake yi.

Kara karanta wannan

Bidiyon dubban mutane da suka tari Sarkin Kano bayan Juma'a, ya aika sako a huduba

Dubban mutane sun tarbi Aminu Ado bayan sallar Juma'a a Kano
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya samu tarba daga Kanawa bayan sallar Juma'a. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Kano: Kanawa sun tarbi Aminu Ado Bayero

A faifan bidiyon wanda Masarautar Kano ta wallafa a shafin X, an gano dubban masoya tare da Aminu Ado.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makon da ya gabata ma, Aminu Ado ya gudanar da sallar Juma’a a masallacin fadarsa da ke Nasarawa.

Kotu ta yi zama kan masarautun Kano

Wannan na zuwa ne yayin da ake tsaka da shari’a kan masarautun Kano wanda Majalisar jihar ta rusa.

A jiya Alhamsi 6 ga watan Yuni, kotu ta yi zama kan shari’ar masarautun bayan Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da korafi.

'Dan Agundi ya maka Majalisar Jihar da kuma Gwamna Abba Kabir bayan rushe masaurautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Daga bisani kotun ta dage sauraran shari'ar har zuwa ranar Alhamsi 13 a watan Yuni mai zuwa.

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

Sarkin Gwandu ya taya Sanusi II murna

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Gwandu, Manjo-janar Muhammad Ilyasu Bashir ya taya Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II murna.

Basaraken ya ce samun Sanusi II a matsayin sarki ba karamin ci gaba zai kawo ba ga jihar Kano duba da kwarewarsa.

Hakan ya biyo bayan dawowa da Sanusi II kan karagar mulki bayan tube Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.