Masarautun Kano: Kotu Ta Sanya Lokacin Fara Sauraran Shari'a, Ta Fadi Ka'idar Zama

Masarautun Kano: Kotu Ta Sanya Lokacin Fara Sauraran Shari'a, Ta Fadi Ka'idar Zama

  • Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Kano ta shirya fara sauraran shari'ar da aka shigar kan masarautun jihar
  • Kotun ta sanya yau Alhamis 6 ga watan Yuni domin fara sauraran karar da aka dage saboda yajin aikin kwadago
  • Hakan ya biyo bayan maka Gwamna Abba Kabir a kotu bayan rushe masarautun da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Kotu ta sanya ranar fara sauraran shari'ar da aka shigar kan rigimar masarautun jihar Kano.

Kotu ta zabi yau Alhamis 6 ga watan Yuni domin sauraren shari'ar ta manhajar Zoom.

Kotu ta fara sauraran shari'ar masarautun Kano a yau Alhamis
Babbar Kotun Tarayya ta fara sauraran shari'ar da aka shigar kan rushe masarautun Kano. Hoto: Masarautar Kano.
Asali: Twitter

Kano: Kotu ta fara zama kan masarautu

Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari'a, A.A Liman za ta fara jin bahasin bangarorin biyu, cewar Aminiya.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Halin da ake ciki a Kano yayin da kotu ta fara zaman shari'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba, kotun ta sanya Litinin 3 ga watan Yuni a matsayin ranar fara sauraran karar wadda aka dage sakamakon yajin aikin kungiyoyin Kwadago.

Daya daga cikin manyan hakimai a fadar Kano, Sarkin Dawaki Babba, Alh. Aminu Babba Dan Agundi wanda kuma Hakimin Nassarawa ne shi ya shigar da karar a gaban kotun, cewar New Telegraph.

An maka Majalisa, gwamnan Kano a kotu

Dan Agundi yana kalubalantar Majalisar Dokokin jihar da Gwamna Abba Kabir kan rushe masarautun jihar 5 da gwamnatin Ganduje ta kirkiro.

Hakan ya biyo bayan tabbatar dadakiar rushe masarautun da Majalisar jihar ta yi yayin da Abba Kabir yasa ya mata hannu.

Daukar wannan mataki ya kawo rigima a jihar kan ainihin wanene sahihin sarki tsakanin Aminu Ado Bayero da kuma Muhammadu Sanusi II.

An dage zaman shari'ar masarautun Kano

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: NLC ta kawo babban cikas a a kotu kan rigimar sarautar Kano

A wani labarin kun ji cewa yajin aikin da ma'aikata suka fara yau Litinin 3 ga watan Yuni ya kawo tsaiko a ci gaba da sauraron shari'a kan masarautar Kano.

Manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani biyo bayan gaza cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi da ƙarin kuɗin wuta.

Hakan ya biyo maka Majalisar jihar da Abba Kabir da aka yi kan rushe masarautu biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.