"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

"Dalilin da ya sa har yanzu Aminu Ado Bayero yake halastaccen Sarkin Kano"

  • Wani lauya a jihar Kano, Umar Sa'ad Hassan, ya yi bayanin cewa har yanzun Alhaji Aminu Ado Bayero ne halastaccen Sarkin Kano
  • Hassan ya bayyana cewa babbar kotun tarayya mai zama a jihar ta ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi kan sarauta
  • A wata hira da Legit Hausa, Hassan ya ce Aminu ne Sarkin Kano har sai lokacin da gwamnatin jihar ta ɗaukaka ƙara kuma aka jingine umarnin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wani kwararren mai shiga tsakani kuma masanin doka, Umar Sa'ad Hassan ya ce har yanzu Aminu Ado Bayero ne Sarkin Kano a doka.

Umar Sa'ad Hassan ya bayyana cewa sarki na 15, Alhaji Amunu Ado Bayero ne halastaccen sarkin Kano ba Muhammadu Sanusi II ba.

Kara karanta wannan

Kano: Hakimai na cigaba da yiwa Sanusi II mubaya'a duk da barazanar umarnin Kotu

Muhammadu Sanusi, Abba Kabir da Aminu Ado Bayero.
Lauya ya yi bayanin cewa har yanzu Aminu Ado ne sarkin Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya yi bayanin cewa babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta bayar da umarnin a dakatar da sabuwar dokar masarauta wadda majalisar dokokin jihar ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya ƙara da cewa kotun ta kuma dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi II a kan karagar Sarkin Kano.

Wanene sarkin Kano a yau a doka?

A cewar Umar, Sarki Aminu Ado na nan a matsayin basaraken birnin Kano har sai lokacin da gwamnatin jihar ta ɗaukaka ƙara kuma kotu ta soke umarnin.

Umar ya ce ƙarar da gwamnatin Kano ta kai kotu da ke da iko iri ɗaya da babbar kotun tarayya cin mutuncin shari'a ne.

A wata hira da Legit.ng, lauyan ya ce:

"Babban Kotun Tarayya ta dakatar da amfani da sabuwar dokar masarautar da kuma sake mayar da Sanusi II.
"Duk wanda ke da korafi ko wane iri ne ya je kotun ko kuma ya daukaka kara ba wai ya nemo wani umarnin daga kotu mai daraja daidai da wannan ba.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauya ya feɗe gaskiya, ya nemowa Aminu Ado da Sanusi II mafita

"Hakan rashin mutunta kotu ne kuma matakin da alkalin alƙalan Najeriya ya ɗauka shi ne daidai. Maganar gaskiya Aminu Ado ne Sarkin Kano yanzu haka."

A karshe ya ce tun da tsagin Aminu Bayero ne suka shigar da ƙarar, dole ne sai kotu ta tabbatar kuma ta amince da mayar da Sanusi kafin ya iya zama sarkin Kano.

Yan sanda da batun sallar Sarkin Kano

A wani rahoton kuma jita-jitar da ake yadawa cewa sarkin Kano na 14, Aminu Bayero ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin fada ba gaskiya ba ne

Rundunar 'yan sandan Kano ta nemi jama'a da suyi watsi da wannan jita-jitar tana mai cewa Aminu Bayero zai yi Juma'a ne a karamar fadar Nasarawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262