An Zargi Wani Jami'in KEDCO da Kashe Abokinsa Saboda Abin Duniya

An Zargi Wani Jami'in KEDCO da Kashe Abokinsa Saboda Abin Duniya

  • An shiga alhini a Gama dake jihar Kano bayan wani mai suna Sadiq ya yaudari abokinsa Bello Bukar Adamu tare da kashe shi har lahira da yammacin Lahadi
  • Abdullahi Abubakar, kanin marigayin ya shaida cewa Sadiq ya kira yayansa da yammacin Lahadi yana masa albishir din samun aikin da ya dade yana nema
  • Bello Bukar Adamu wanda ke aiki da makashinsa a kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na neman aiki a hukumar tattara kudin shiga ta tarayya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano-An shiga jimami a unguwar Gama B da ke jihar Kano bayan an tsinci gawar wani magidanci, Bello Bukar Adamu a karamar hukumar Kumbotso.

Kara karanta wannan

Hoto: Yahaya Bello ya sanya kayan mata domin ya tsere daga Najeriya? Gaskiya ta bayyana

Marigayin ya bar gida ne a ranar Lahadi da yamma, bayan wani abokin aikinsa da suke aiki tare a kamfanin rarraba hasken wutar lantarki (KEDCO) ya kira shi da maraice.

Police
Wani aboki ya amsa kashe amininsa a Kano Hoto: Getty images
Asali: Getty Images

Kanin marigayin, Abdullahi Abubakar, a rahoton da Daily Trust ta wallafa ya bayyana cewa yayan na sa ya dade yana neman aiki a hukumar tattara kudin shiga ta tarayya (FIRS).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mutumi ya ce bayan sun gama wayar da Sadiq ne yayansa, Bello Bukar ya dauki mubudin motarsa ya bar gida.

“Amininsa ya kashe shi,” Abdullahi

Abdullahi Abubakar, cike da takaicin ya bayyana cewa tun ranar Lahadi da yayansa ya fita ya hadu da abokinsa sadiq bai dawo gid aba.

A cewarsa, Sadiq ya kira shi, tare da yaudararsa da cewa an dace da aikin da yake nema a hukumar FIRS, amma bai sake dawowa gida ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi dalilin fara rajistar gawan da ake birnewa a makabartu

An tsinci gawarsa a Kumbotso

'Danuwan ya ce sun dade suna cigiya a asibitoci da caji ofis, har ma sun fara jiran kiran masu garkuwa da mutane, sai aka gani gawarsa a bayan wani layi a Kumbotso.

Da aka zurfafa bincike sai abokin ya shaidawa jami’an tsaro cewa da shi aka kashe Bello Bukar Adamu, amma har yanzu ba a gano sauran da ake zargi da kisan ba.

Abdullahi Abubakar, ya kara da cewa suna cike da takaicin kasancewar Sadiq Abokin marigayin ne sosai.

Rundunar yan sandan Kano ta tabbata da cewa ana zurfafa bincike kan lamarin.

Wani ya kashe abokinsa a Lagos

Mun ruwaito muku a baya yadda al'umma suka shiga fargaba bayan wani aboki, Emma ya sokawa abokinsa White London kwalba saboda ya ki ba shi N100.

Hatsaniya ta kaure tsakanin abokan biyu ne bayan White London ya ranci kudi daga wajen Emma amma ya gaza biyansa a lokacin da ya nema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel