Kamfanin KEDCO ya Yanke Wutar Asibitin Kano, Masu Haihuwa Suna Kwance

Kamfanin KEDCO ya Yanke Wutar Asibitin Kano, Masu Haihuwa Suna Kwance

  • Ma'aikatan kamfanin rarraba hasken wuta a Kano (KEDCO) sun yanke wutar asibitin Imamu Wali biyo bayan sabani da mahukuntan asibitin
  • Yanke wutar ya sanya wasu yada labarin cewar akwai fargabar mutane 4 sun rasa rayukansu, lamarin da hukumar HMB ta ce ba gaskiya ba ne
  • Hukumar ta bayyana cewa tana biyan kudin wutan N300, 000 duk wata, kuma za ta dauki matakan gyara, amma yanzu an sayi man dizel a asibitin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano-Ma’aikatan kamfanin rarraba hasken wuta ta KEDCO sun yanke wutar asibitin Imamu Wali wanda ya janyo fargabar rasuwar marasa lafiya guda 4.

Kara karanta wannan

Ganduje: An sake bankado yadda tsohon gwamnan ya karkatar da N51.3bn, an gano dalili

Tuni hukumar kula da manyan asibitoci ta Kano ta musanta cewa an samu rashin rai a daidai lokacin da ta bayyana takaicin yadda KEDCO ta yanke wutar.

Yanke wutar da KEDCO ta yi ya jawo fargabar rasuwar wasu marasa lafiya
KEDCO ta yanke wutar asibitin Imamu Wali a Kano Hoto: UGC
Asali: UGC

A sanarwar da kakakin hukumar, Samira Suleima ta aikewa manema labarai wanda Legit Hausa ta gani, hukumar ta ce ta na da sola wanda aka yi amfani wajen haska asibitin bayan KEDCO ya yanke wutar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce bai kamata a ce sabani kadan ya janyo KEDCO su yanke wutar da ake kula da marasa lafiya a asibitin ba.

“Muna biyan kudin wuta,” Dakta Mansur

A wani sakon murya da shugaban kula da manyan asibitoci na Kano, Dakta Mansur Mudi ya fitar, ya ce asibitin Imamu Wali na biyan kudin wuta Naira dubu 300 duk wata.

Dr. Mansur ya bayyana cewa:

Kara karanta wannan

CAC: Hukumar kula da kamfanoni ta Najeriya na daukar aiki? Gaskiya ta bayyana

“Amma saninmu ne cewa wutan nan ba samuwa ta ke ba, sannan kuma an kara kudinta.
Wannan mutane da su ke kula da asibitin suna biyan kudin wuta duk wata dubu 300. Amma yanzu an kawo bill an ce akwai na baya da ake bi N1.8m."

Ya kara da cewa yanzu haka sun bayar da umarnin a sayo man dizel domin ci gaba da gudanar da ayyukan ceton rai a asibitin, yayin da su ke kokarin warware matsalar wutar.

An samu karancin wuta a Najeriya

A baya kun ji yadda karancin hasken wutar da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ke bayarwa ya jawo karuwar tsadar kankara a lokacin azumin watan Ramadan da ya gabata.

A jihar Kaduna, an samu wauraren da ake sayar da jakar ruwan sanyi kan naira dari 400 zuwa dari 500.

Asali: Legit.ng

Online view pixel