Ke duniya: Aboki ya kashe abokinsa a kan N100

Ke duniya: Aboki ya kashe abokinsa a kan N100

Wani mutum mai suna Emma ya sokawa abokinsa mai suna White London wuka a Legas saboda naira dari. Lamarin ya faru ne wajen karfe 11 na daren Laraba a Whitesand da ke yankin Badia da ke Apapa a jihar Legas.

White London dai ya ranta kudin Emma ne da alkawarin zai biya shi a cikin satin. Amma kuma sai ya kasa biyan kudin wanda hakan ya fusata Emma din, kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Wani wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce fada ne suka fara kuma Emma yafi karfinsa. Hakan yasa White London ya fasa kwalba tare da sukar wanda ke bin shi bashi a hannu.

Ke duniya: Aboki ya kashe abokinsa a kan N100
Ke duniya: Aboki ya kashe abokinsa a kan N100
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Abinda Zulum ya faɗa a kan ziyarar da Buhari ya kai Borno

“A jike da jini, Emma ya dauka fasasshiyar kwalbar ya sokawa White London a wuya. Kwalbar ta shiga sosai cikin wuyan shi har muka fara ganin wani farin abu. Saboda yawan jinin da ya zubar, a take ya ce ga garinku,” shaidar ta sanar.

Wanda ake zargin yayi kokarin gudu amma sai mazauna yankin suka kama shi tare da mikawa ‘yan sanda.

‘Yan sanda da suka isa wajen abinda ya faru sun dauke gawar inda aka kai ta asibiti don adanawa.

Kamar yadda rundunar ‘yan sandan ta sanar, an mayar da wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar don ci gaba da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: