Yaki da Ta’addanci: Ma'aikatar Tsaro Ta Rabawa Sojoji Sababbin Motocin Yaki Masu Sulke

Yaki da Ta’addanci: Ma'aikatar Tsaro Ta Rabawa Sojoji Sababbin Motocin Yaki Masu Sulke

  • Ma'aikatar tsaro ta sayo sabbin motocin yaki masu sulke (APC) guda 20 tare da mika su ga hedikwatar tsaro a ranar Laraba, 8 ga Mayu
  • Kakakin hedikwatar, Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce motocin na da karfin fasahar hango abokan gaba daga nesa tare da farmakarsu
  • Gusau ya kara da cewa wani kamfanin Najeriya ne ya hada motocin wanda hakan zai bunkasa masana'antun cikin gida da rage kashe kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Laraba ne babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Christopher Musa, ya karbi sabbin motocin yaki masu sulke guda 20 domin bunkasa yaki da 'yan ta'adda.

Ma'aikatar ta ba sojoji sababbin motocin yaki masu sulke
Hedikwatar tsaro ta karbi sababbin motocin yaki masu sulke guda 20. Hoto: NAN
Asali: UGC

Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito mukaddashin daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya sanar da hakan a ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisar wakilai ta ki daukar matsaya kan harajin tsaron yanar gizo, 'dan majalisa ya koka

Sojoji sun samu motocin yaki na zamani

Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce an yi jigilar motocin ne a wani takaitaccen biki da babban sakataren ma’aikatar tsaro, Dakta Ibrahim Kana ya yi a madadin ministan tsaro, Alhaji Mohammed Badaru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojan ya ce motocin sulken na zamani ne da ke dauke da ingantattun makamai da tsarin sadarwa mai karfi wanda zai iya gano abokan gaba daga nesa da kuma kai masu farmaki.

A cewarsa, za su kuma ba da damar gudanar da ayyukan soji ba tare da wata matsala ba, kuma wani kamfanin Najeriya ne ya samar da motocin, kafar yada labarai ta NAN ta ruwaito.

"A Najeriya aka hada motocin" - Gusau

Babban sakataren ya bayyana cewa dabarar da aka yi ta baiwa masana’antun cikin gida kwangilar kera motocin ci gaba ne mai kyau.

Kara karanta wannan

Harajin CBN: Na hannun daman Tinubu ya fadi abin da 'yan Najeriya ya kamata su yi

Ya kara da cewa hakan zai ceto kasar daga kashe makudan kudade, samar da ayyukan yi da kuma rage dogaro da kudaden waje.

Babban hafsan tsaro ya magantu

Jaridar The Nation ta ruwaito CDS Janar Musa ya godewa ministan tsaro tare da yin alkawarin yin amfani da sabbin motocin ta yadda ya kamata.

Ya kara da cewa, ko shakka babu motocin za su kara habaka ayyukan da sojoji ke yi na kawar da matsalar rashin tsaro a kasar.

An yi garkuwa da mutane 13 a Abuja

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun sake kai hari Abuja inda wannan karon suka yi garkuwa da mutane akalla 13.

An tattaro cewa 'yan bindigar sun nemi Naira miliyan 900 kudin fansar mutanen da suka sace yayin da jami'an tsaro suka ce suna bakin kokari domin kwato mutanen.

Asali: Legit.ng

Online view pixel