Ebrahim Raisi: Shugaban Kasar Iran Ya Rasu a Hatsarin Jirgin Sama

Ebrahim Raisi: Shugaban Kasar Iran Ya Rasu a Hatsarin Jirgin Sama

  • Shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya gamu da ajalinsa sakamakon wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya ritsa da shi
  • Ebrahim Raisi ya rasu ne tare da wasu jami'an gwamnatin ƙasar ciki har da ministan harkokin ƙasashen wajen ƙasar da matuƙan jirgin
  • Hatsarin jirgin wanda ba a tabbatar da maƙasudin faruwarsa ba ya auku ne a ranar Lahadi lokacin da shugaban ƙasar ke kan hanyar komawa birnin Tehran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Iran - Shugaban ƙasar Iran, Ebrahim Raisi, ya rasa ransa a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ranar Lahadi.

Hatsarin jirgin wanda ya ritsa da wasu jami'an gwamnatin ƙasar ya yi sanadiyyar rasuwar dukkanin mutanen da ke cikin jirgin mai saukar ungulu.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da shugaban kasar Iran ya samu matsala, ya yi muguwar saukar gaggawa

Shugaban Iran ya rasu
Ebrahim Raisi ya rasu a hatsarin jirgin sama Hoto: Sakineh Salimi/Borna News/Aksonline ATPImages
Asali: UGC

Iran: Yaushe Ebrahim Raisi ya rasu?

Jaridar CNN ta kawo rahoto cewa jami'ai ne suka tabbatar da rasuwar Ebrahim Raisi da sauran mutanen da hatsarin ya ritsa da su a safiyar ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin mai saukar ungulu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Tehran daga Tabriz, ya faɗo ne a ranar Lahadi.

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai, Shugaba Ibrahim Raisi da ministan harkokin wajen ƙasar, Hossein Amir Abdollahian.

Sannan akwai gwamnan lardin gabashin Azerbaijan Malek Rahmati, Imam Mohammad Ali Alehashem na Tabriz.

Sauran sun haɗa da matuƙan jirgin, shugaban ma'aikatan jirgin da kuma shugaban tsaro da dogari, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Raisi: An tabbatar da rasuwar shugaban Iran

Shugaban ƙungiyar agaji ta Red Crescent ya tabbatar da rasuwar mutanen.

A kalamansa:

"Jami’an ceto sun isa wurin ragowar jirgin mai saukar ungulu. Bayan gano wurin da jirgin mai saukar ungulu ya faɗo, ba a ga alamun mutanen da ke cikinsa na raye ba."

Kara karanta wannan

"Mu taimaka masu," Ganduje ya yi magana kan mummunan harin da aka kai Masallaci a Kano

Rikicin kasar Israila da Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Iran ta harba makaman ba da kariya bayan an ji ƙasar fashewar wasu abubuwa a yankin Isfahan na ƙasar.

Ana zargin dai ƙasar Israila ce ta kai hari a Iran yayin da dangantaka ke ƙara tsami tsakanin ƙasashen biyu na yankin Gabas ta Tsakiya masu gaba da juna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng