Rundunar soji ta kaddamar da wasu sabbin motoccin yaki 4 da aka kera a Najeriya (Hotuna)
Rundunar Sojojin Najeriya ta kaddamar da sabbbin motoccin yaki wadanda nakiya baya fasa su guda hudu da aka kera a Najeriya da hadin gwiwar Proforce Limited domin taimakawa sojoji yaki da ta'addanci.
Shugaban hafsin sojojin kasar Najeriya Laftanat Janar Tukur Buratai yana daya daga cikin manyan bakin da suka hallarci taron kaddamar da sabbin motocin yakin.
Proforce Limited kamfanin Najeriya ne da ya kware wajen kerawa da inganta motocin yaki iri daban-daban har da wadanda nakiya ba ta iya fasa su.
DUBA WANNAN: An gano wuri da aka birne sojoji fiye da 1000 da Boko Haram suka kashe - Rahoto
An rada wa motar sunan 'Thunder' wadda ke nufin tsawa saboda ingancin ta ba karko musamman a filin daga. An fara kadamar da motar ne a shekarar 2017 amma daga bisani aka sake komawa domin inganta tsarin.
An fara aikin inganta motocin yakin ne saboda halin da sojojin Najeriya ke ciki ne yaki da 'yan ta'addan da suke adabar wasu sassa na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun kwashe kimanin shekaru bakwai suna fafatawa da 'yan ta'addan hakan ya sa su kayi shawarar canja salo da dabarun yaki daga amfani da tsohuwar motar Toyota zuwa sabbin motoccin yaki daga kasashen waje. Hakan ya sa aka fara kera motocin a gida Najeriya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng