Yaki da ta’addanci: Rundunar Soja ta aika da wasu manyan motocin yaki jahar Borno (Hotuna)

Yaki da ta’addanci: Rundunar Soja ta aika da wasu manyan motocin yaki jahar Borno (Hotuna)

Rundunar Sojan Najeriya ta aika da wasu sababbin motocin yaki guda hudu na musamman zuwa bakin daga a yankin Arewa maso gabashin Najeriya don kara ma yaki da yan ta’addan Boko Haram kaimi.

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ne ya kaddamar da wadannan motoci, wandanda basa jin bom, kuma harin kwantan bauna ba zai musu illa ba, kamar yadda ya bayyana.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun hana likitoci su duba mu a asibitin kasar Indiya - Zakzaky

Yaki da ta’addanci: Rundunar Soja ta aika da wasu manyan motocin yaki jahar Borno (Hotuna)
Yaki da ta’addanci: Rundunar Soja ta aika da wasu manyan motocin yaki jahar Borno (Hotuna)
Asali: Facebook

Buratai wanda ya samu wakilicin shugaban sashin horas da Sojoji da muhimman ayyuka na rundunar, Enobong Udoh ya kaddamar da motocin ne a ranar Talata a garin Maigumeri na jahar Borno, inda yace motocin zasu taimaka ma Sojoji wajen yaki da yan ta’adda.

A watan Yulin data gabata ne shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Janar Abayomi Olanisakin ya karbi motocin bayan an kammala kerasu. Bugu da kari, Burarai ya shaida ma Sojoji cewa idan basu sa himman kawo karshen yaki da Boko Haram ba, motocin ba za su amfanesu ba.

Yaki da ta’addanci: Rundunar Soja ta aika da wasu manyan motocin yaki jahar Borno (Hotuna)
Yaki da ta’addanci: Rundunar Soja ta aika da wasu manyan motocin yaki jahar Borno (Hotuna)
Asali: Facebook

“Don haka dole ne ku kasance masu himma wajen gudanar da ayyukanku, tare da jajircewa wajen kawo karshen yaki da ta’addanci cikin kankanin lokaci, ina tabbatar muku zamu cigaba da horas da Sojoji tare da kulawa da walwalarsu.” Inji shi.

Haka zalika Buratai ya jinjina ma Sojoji bisa jarumtar da suke nunawa a bakin daga, wanda yace wannan ne dalilin nasarar da ake samu a kan mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Shima da yake nasa jawabin, babban kwamandan rundunar Sojoji ta musamman, Mhoundayi Ali ya bayyana gamsuwarsa da samun motocin nan, inda yace zasu basu kwarin gwiwar gamawa da Boko Haram da ragowar ISWAP.

Daga karshe, kwamanda Ali yace ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen farautar shuwagabannin Boko Haram da mayakansu har sai sun ga bayansu gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel