Ministar Tinubu da Uba Sani Za Su Halarci Muhimmin Taro a Birnin Landan

Ministar Tinubu da Uba Sani Za Su Halarci Muhimmin Taro a Birnin Landan

  • Doris Nkiruka Uzoka-Anite, ministar masana'antu, ciniki da zuba jari za ta halarci taron zuba jari na ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje a birnin Landan
  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da wata tawagar shugaban ƙasa na daga cikin mutanen da za su halarci taron a ranar 24 ga watan Mayu
  • Uba Sani zai kasance babban mai jawabi a wajen taron wanda zai samu halartar shugabannin ƴan kasuwa na ƙasashen waje da ƙasashen Afirika

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministar masana’antu, ciniki da zuba jari, Doris Nkiruka Uzoka-Anite, za ta kasance babbar baƙuwa ta musamman a wurin taron zuba jari na ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje (NDDIS).

Kara karanta wannan

'Mutuwar' wani matashi Kabiru sakamakon azabtarwar ƴan sanda ya tada ƙura a Najeriya

Masu shirya taron da za a gudanar a ranar, 24 ga watan Mayu a birnin Landan suka tabbatar da hakan.

Uba Sani zai halarci taro a Landan
Doris Anite da Gwamna Uba Sani za su halarci taron zuba hannun jari a Landan Hoto: @DrDorisAnite, @ubasanius
Asali: Twitter

Me gwamna Uba Sani zai yi a taron?

Taron mai taken 'Invest Nigeria, Invest Africa' zai samu halartar gwamnan jihar Kaduna Uba Sani a matsayin babban mai jawabi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran mahalarta taron sun haɗa da babbar mai ba shugaban ƙasa shawara kan samar da ayyukan yi da ƙananan sana'o'i, Temitola Emitola Adekunle Johnson.

A tawagar akwai shugabar hukumar ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje, Hon. Abike Dabiri Erewa.

A cewar sanarwar da daraktan yaɗa labarai ta ƙungiyar, Lady Doyin Ola ta fitar, taron zai samu halartar shugabannin ƴan kasuwa na ƙasashen waje da ƙasashen Afirka, Birtaniya, da ƙasashe rainon Ingila da sauran masu zuba hannun jari.

Za a ba da bashi kyauta

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa na ƙona mutane suna sallah a Kano," Wanda ake zargi ya faɗi gaskiya

Tun da farko wanda ya kafa NDDIS, Prince Bimbo Roberts Folayan, ya ce sun samu ci gaba a tattaunawar da suke yi da waɗanda za su ɗauki nauyin shirin ta hanyar ba da kaso 100% na bashin da ba za a biya ba, cewar rahoton Independent.

"Na yi matukar farin ciki sosai game da taron na bana domin a karon farko, za mu shiga cikin aikin tantance ayyukan sannan kuma za mu taimaka wajen tura ayyukan da suka cimma muradun SDG domin samun tallafi.
"Wannan dai shi ne karon farko da aka ba mu wannan dama tun lokacin da muka fara jawo ayyuka a Najeriya da Afirika."

- Prince Bimbo Roberts Folayan

Doris Anite ta gana da Gwamna Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gana da ministar masana'antu, ciniki da zuba jari, Doris Anite a birnin Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 50, sun sace mutane sama da 500 a Arewa

Gwamnan ya gana da ministar ne domin nemo hanyoyin bunƙasa kasuwanci a jihar wacce ta kasance cibiyar kasuwanci musamman a Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng