Majalisar Wakilai Ta Ki Daukar Matsaya Kan Harajin Tsaron Yanar Gizo, 'Dan Majalisa Ya Koka

Majalisar Wakilai Ta Ki Daukar Matsaya Kan Harajin Tsaron Yanar Gizo, 'Dan Majalisa Ya Koka

  • Dan majalisa Manu Soro daga jihar Bauchi ya gabatar da kuduri a gaban majalisar wakilai na bukatar soke harajin tsaron yanar gizo
  • Manu Soro ya ce kakaba sabon haraji a irin wannan yanayi na kalubalen tattalin arziki zai kara jefa ‘yan kasar cikin tsadar rayuwa
  • Sai dai kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, ya ki karbar kudirin tare da shawartar Soro ya dan dakata shugabannin majalisar sun tattauna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A jiya ne kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ki karbar kudirin da aka gabatar na bukatar dakatar da harajin tsaron yanar gizo.

An gabatar da kudurin soke harajin tsaron yanar gizo a majalisar wakilai
Kakakin majalisar wakilai, ya yi fatali da kudurin soke harajin tsaron yanar gizo. Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Legit Hausa ta ruwaito cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya umurci dukkanin bankunan kasar da su fara cire 0.5% daga hada-hadar kudaden abokan hulda.

Kara karanta wannan

"7.5% ya yi kadan": Gwamnatin Tinubu za ta ƙara harajin VAT, a canja tsarin raba kudi

Kungiyar kwadago ta yi watsi da wannan harajin, inda ta bayyana shi a matsayin wani karin nauyi a kan 'yan Najeriya, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan majalisa ya gabatar da kuduri

A zaman majalisar na ranar Laraba, Hon. Manu Soro daga jihar Bauchi ne ya gabatar da kudirin, inda ya nuna damuwarsa kan yadda harajin zai kara jefa mutane a matsin tattali.

Soro ya kara da cewa kakaba sabon haraji a wannan yanayi na kalubalen tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, zai kara jefa ‘yan kasar cikin tsadar rayuwa da tsadar abinci.

"Kuduri bai karbu ba" - Kakakin majalisa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Soro ya yi kira ga majalisar da ta sa bankin CBN ya janye daftarin harajin tsaron yanar gizo tare da dakatar da aiwatar da shi cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi watsa watsa da Gwamnatin Bola Tinubu saboda lafta harajin 0.5% a banki

Ya kuma bukaci Ministan kudi da ya guji bullo da sabbin haraji ko kara kudin harajin da ake da su har sai yanayin tattalin arzikin kasar ya inganta sosai.

Sai dai kakakin majalisar Abbas ya takawa Soro burki, ya ce wannan kuduri bai karbu ba yayin da ya bukaci Soro ya ba shugabannin majalisar damar tattaunawa kan lamarin.

Haraji: Peter Obi ya caccaki gwamnatin Tinubu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi ya caccaki gwamnatin tarayya kan bullo da harajin tsaron yanar gizo.

Peter Obi ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da bullo da tsare-tsare da za su kara jefa 'yan Najeriya a mawuyacin halin da suka shiga tun bayan janye tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.