Kalli wasu motocin yaƙi da rundunar Sojin Najeriya ta ƙera da kanta

Kalli wasu motocin yaƙi da rundunar Sojin Najeriya ta ƙera da kanta

Rundunar Sojin Najeriya ta kera wasu motocin yaki a gida Najeriya da zasu taimaka mata a yakin da take yi da take yi da yan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin kasar nan.

Ministan tsaro, Masur Dan Ali ne ya kaddamar da motocin a yayin bikin daura tubalin ginin sabon barikin Sojoji mai suna Muhammadu Buhari a garin Giri, dake babba birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Sabon Sakataren gwamanti ya jadda bukatar gyara a gwamnatin shugaba Buhari

Kalli wasu motocin yaƙi da rundunar Sojin Najeriya ta ƙera da kanta
Motocin

Shugaban hafsoshin rundunar sojan kasa, Laftanar janar Turkur Yusuf Buratai ya bayyana cewa masana da kwararrun jami’an rundunar ne suka kera motocin bayan kwashe tsawon lokaci suna gudanar da bincike.

Kalli wasu motocin yaƙi da rundunar Sojin Najeriya ta ƙera da kanta
Sanya tubalin

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buratai yana fadin, matakin da rundunar Soji ta dauka na kera kayan yakinta da kanta zai taimaka kwarai wajen kakkabe ragowar yan Boko Haram da suka rage.

Wani shafi a kafar sadarwa zamani ta Facebook, mai suna ‘Support the Nigerian Military’ data daura hotunan motocin yakin ta bayyana cewa tuni aka tura wasu daga cikin motocin filin daga, don agaza ma Sojoji.

Kalli wasu motocin yaƙi da rundunar Sojin Najeriya ta ƙera da kanta
Motocin

Buratai yace motocin yakin na daga cikin makaman da aka gwada su yayi gasar sarrafa kananan makamai daya gudana a dajin Sambisa a shekarar nan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Luguden wuta a kan yan Boko Haram, kalla Legit.ng TV

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng