An Soki Yadda Bola Tinubu Ya Kare Shekaran Farko a Kan Mulkin Najeriya

An Soki Yadda Bola Tinubu Ya Kare Shekaran Farko a Kan Mulkin Najeriya

  • Yayin da ake fara shirye-shirye bikin cika shekara guda a mulkin Bola Tinubu, masana sun fara tofa albarkacin baki kan mulkinsa
  • Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa cikin shekara 1 shugaban kasar bai tsinana komai ba sai kara jefa al'umma cikin wahala
  • Har ila yau Farfesan ya bayyana yadda gwamnatin tarayya karkashin Tinubu ta dawo mai tatsan yan kasa da sunan karbar haraji

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Najeriya - Wani daga cikin dattawan Arewa, Farfesa Usman Yusuf ya koka kan yadda mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu ja kawo ci baya a Najeriya.

Shugaba Tinubu
Farfesa Usman Yusuf ya ce Tinubu ya gagara komai cikin shekara guda. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Gidan talabijin din Channels ya ruwaito Farfesan na cewa maimakon ceto yan Najeriya Tinubu ya kara tsundumasu cikin wahala.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Mulkin Tinubu: Halin da mutane ke ciki

Farfesa Usman Yusuf ya ce a halin yanzu yan kasa sun fita daga hayyacinsu saboda wahalar rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin takaici ne yadda aka mayar da yan Najeriya suna layin karbar abinci kamar masu yawon bara.

Cikar Tinubu shekara a kan mulki

Yayin da ake shirye-shirye cikar Bola Tinubu shekara daya a kan mulki, Farfesa Usman ya ce babu abin da shugaban kasar ya yi sai kara yaudara da cin amana.

Farfesan ya kara da cewa cikin mako mai zuwa gwamnatin za ta fara farfaganda kan ta inganta rayuwar 'yan kasa amma babu gaskiya a lamarin ta.

Tattalin arziki a zamanin shugaba Tinubu

Har ila yau Farfesa Usman ya ce cikin shakara guda, Tinubu ya gagara taɓuka komai kan habaka tattalin arziki.

A cewarsa, abin da Tinubu ya yi nasar a kai kawai shi ne jefa yan Najeriya cikin talauci da karayar arziki, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

"Yana hawa Najeriya ta durkushe": Tsohon Sakataren Gwamnatin Buhari ya soki Tinubu

Ya kara da cewa gwamnatin ta zama mai tatsar yan kasa da sunan haraji maimakon nemo mafita ga matsalolin da suka addabi kasar.

Farfesa Usman Yusuf ya bayyana haka ne yayin hira da tashar a jiya Lahadi, 19 ga watan Mayu.

An koka kan satar dalibai a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa ta yi kakkausar magana kan satar yara ɗalibai a yankin Arewa, tana mai cewa "ya isa haka".

Farfesa Ango Abdullahi, shugaban kungiyar dattawan Arewa, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta hannun Abdul-Azeez Suleiman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel