Sojin Najeriya sun fara hada motoci da makaman yaki

Sojin Najeriya sun fara hada motoci da makaman yaki

-Kamfanin kere-kere na hukumar sojin Najeriya ta kera kananan motocin yaki

-Shugaban sojojin kasa, Janar Burutai ne ya bayyana haka a lokacin da yake duba yadda ake kera motocin

-Burutai ya bayyana cewa kamfanin zai fara kera motocin masu yawa don ganin an magance matsalolin tsaro da ake fama da su cikin kasa

Hukumar sojin Najeriya ta ce kanan motoci da makaman yaki da kamfaninta ke hadawa zai taimka wajen magance matsalolin tsaro na cikin gida Najeriya

Shugaban sojojin sama, Lt-Gen Tukur Burutai ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da yan jarida a ranar Alhamis bayan da ya duba yadda kamfanin ke kera kayan yakin a farfajiyar kamfanin dake a Rigachikun karamar hukumar Igabi jihar Kaduna.

Burutai ya bayyana cewa za a nuna kashin farko na kananan motocin da kayan yakin da kamfanin ya hada a ranar 6 ga watan Yuli na wannan shekarar

KARANTA WANNAN: Garuruwa biyar da mata ke auren fiye da namiji guda

Burutai ya bayyana cewa tun cikin shekarun 1960s, babu wata hubbasa wajen ganin cewa an rinka hada kayan yaki a cikin Najeriya.

Ya ce “Wannan wani babban cigaba ne, kuma muna cikin lokaci. Muna aiki wajen ganin an hada motocin masu yawa.

“Motocin zasu taimaka mana wajen magance matsalolin tsaro da ake fama dasu a Najeriya. Na san kowa na damuwa da matsalolin tsaron da ake fama dasu.

“Amma abun takaici shekara da shekaru, tun cikin 60s ba muyi wata rawar azo a gani ba wajen hada kayan yaki cikin gida.

“Ina tunanin idan wannan kamfanin ya fara aiki, kamar yadda muke tsammani, to zamu kasance munyi abu mai kyau a matsayinmu na kasa.” A cewarshi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng