Kakakin Majalisa Ya Ba Ganduje Mafita Wajen Warware Rikicin Jam'iyyar APC

Kakakin Majalisa Ya Ba Ganduje Mafita Wajen Warware Rikicin Jam'iyyar APC

  • Kakakin majalisr wakilai, Abbas Tajudeen ya yi magana kan rikicin cikin gida da ke damun ƴaƴan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
  • Abbas ya buƙaci shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da ya kafa kwamitocin sulhu waɗanda za su sasanta ƴaƴan jam'iyyar ta APC
  • Kakakin majalisar ya yi nuni da cewa akwai rikice-rikice na cikin gida tsakanin ƴaƴan jam'iyyar a jihohi da dama waɗanda akwai buƙatar a sasanta su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya ba shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, shawara kan rikicin jam'iyyar.

Abbas Tajudeen ya buƙaci Ganduje da ya kafa kwamitocin sulhu da za su haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar da ke rikici da juna a faɗin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Atiku da Obi na shirin haɗa kai, ƙungiya ta faɗi wanda ƴan Najeriya za su zaɓa a 2027

Abbas Tajudeen ya ba Ganduje shawara
Abbas Tajudeen ya bukaci Ganduje ya kafa kwamitocin sulhu a APC Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Kakakin majalisar ya bayar da shawarar ne a yayin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kaduna a ranar Lahadi, 19 ga watan Mayun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abbas ya yi nuni da cewa wasu ƴaƴan jam’iyyar APC sun fusata, domin haka akwai buƙatar a sasanta da su ta yadda jam'iyyar za ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Wace shawara Abbas ya ba Ganduje?

"Ina so in yi kira ga shugaban jam’iyyar na ƙasa da shugabannin jam’iyyar mu da su tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ƴaƴan jam’iyyar. Akwai matsaloli da dama a jihohi daban-daban, a kowace ƙaramar hukuma."
"Lokaci ya yi da za a ja layi. An kammala zaɓe, wannan lokacin mulki ne. Mu manta da abin da ya faru, mu gafarta wa juna sannan mu rungumi juna."
"Ina so in ba da shawara ga shugaban jam'iyyar na ƙasa, da mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa cikin gaggawa, a kafa kwamitocin sulhu."

Kara karanta wannan

Ganduje: Wasu ƴan Arewa sun kunno wuta kan kujerar shugaban APC na Ƙasa

"Sannan kowace jiha ta kafa irin wannan kwamitin sulhu domin mu samar da zaman lafiya da warware rikicin tare da dawo da waɗanda aka yi wa laifi cikin jam'iyyar."

- Abbas Tajudeen

2027: Abbas ya fara zancen tikitin APC

Kakakin majalisar ya kuma buƙaci Ganduje da ya yi amfani da matsayinsa domin ganin an ba ƴaƴan jam’iyyar APC a majalisa da suka yi aiki mai kyau damar sake tsayawa takara a zaɓen 2027, cewar rahoton jaridar The Punch.

A wannan majalisa, an yi watsi da-dama daga cikin wadanda suka goge, sababbin shiga sun samu tikitin tsayawa takara a 2023.

Ganduje ya yabi Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya ce tsare-tsaren Shugaba Bola Tinubu za su inganta Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce a yanzu jam’iyyar APC ta fi kowace samun yawan jihohi da ƙananan hukumomi saboda kyawawan tsare-tsarenta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng