An Bayyana Wanda Zai Zama Sabon Shugaban Kasar Iran Bayan Rasuwar Raisi

An Bayyana Wanda Zai Zama Sabon Shugaban Kasar Iran Bayan Rasuwar Raisi

  • Bayan mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi a hatsarin jirgin sama an bayyana wanda zai hawu kujerarsa domin jagorantar kasar
  • Kundin tsarin mulkin ƙasar ya nuna cewa mataimakin shugaban kasar, Muhammad Mokhber ne zai cigaba da shugabanci a halin yanzu
  • Har ila yau kundin tsarin mulkin ya yi magana kan wani sharadi daya kafin mataimakin shugaban kasar ya hawu kan karagar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Biyon bayan mutuwar shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi a hatsarin jirgin sama an fara maganar wanda zai hau kujerarsa.

IRan Vp
Muhammad Mokhber zai dawo sabon shugaban kasar Iran. Hoto: Islamic Republic of Iran.
Asali: Facebook

A jiya Lahadi ne shugaba Ebrahim Raisi ya samu hatsarin da ya yi sanadiyyar rayuwarsa a lokacin da ake kokarin fara shirin zabe a kasar.

Kara karanta wannan

Abin da muka sani game da hatsarin jirgin sama da ya kashe shugaban Iran

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa mataimakin shugaban kasar Iran, Muhammad Mokhber ne ake tsammani zai rike shugabancin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi

Legit ta ruwaito cewa shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya mutu ne tare da ministan harkokin wajen kasar, Hossein Amir-Abdollahian.

Shuagaban kasar ya yi hatsarin jirgin sama ne yayin da yake kusa da kare shugabancinsa na shekaru hudu.

Me kundin mulkin kasar Iran ya ce?

Kundin tsarin mulkin kasar Iran ya nuna cewa a irin wannan yanayin mataimakin shugaban kasa ne zai cigaba da jagorancin harkokin mulki a kasar.

Sai dai duk da haka mataimakin shugaban kasar zai jira sa hannun shugaban juyin juya halin na kasar, Ayatullah Ali Khamenei.

Yaushe za a yi sabon zabe a Iran?

Bayan mataimakin shugaban kasar ya cigaba da mulki, kundin tsarin mulkin ya tabbatar da cewa za a yi sabon zabe ne cikin kwanaki 50 masu zuwa.

Kara karanta wannan

Jirgin sama dauke da shugaban kasar Iran ya samu matsala, ya yi muguwar saukar gaggawa

Mataimakin shugaban kasar 'dan shekaru 68 an rantsar da shi ne tare da Ebrahim Raisi a watan Agustan shekarar 2021, rahoton the Economic Times.

Amurka ta gargadi Isra'ila kan Iran

A wani rahoton, kun ji cewa a wani sako da ta aikawa Isra'ila, Amurka ta bayyana cewa ba za ta taya Isra'ila yaki da Iran ba idan ta kuskura ta sake tsokano fada.

Har ila yau kasar ta Amurka ta bayyana manyan dalilai kan daukan matakin kin taya Isra'ila yaki da Iran daga cikinsu akwai kaucewa tayar da fitina a gabas ta tsakiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng