Rashin Tsaro: EFCC Za Ta Binciki 'Dan Majalisa Kan Daukan Nauyin Ta’addanci

Rashin Tsaro: EFCC Za Ta Binciki 'Dan Majalisa Kan Daukan Nauyin Ta’addanci

  • Hukumar EFCC ta daura damarar binciken dan majalisar tarayya bisa zargin taimakawa ayyukan ta'addanci a jihar Zamfara
  • Kungiyar matasa mai yaki da cin hanci da rashawa ce ta shigar da korafi ga hukumar a jiya Jumu'a, 17 ga watan Mayu
  • Kakakin kungiyar, Felix Great ya bayyana dalilan da suka sa kungiyar shigar da korafin kan dan majalisar a daidai wannan lokacin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta sha alwashin kama dan majalisar tarayya bisa zargin daukar nauyin ta'addanci.

EFCC Ng
EFCC za ta binciki dan majalisa saboda daukan nauyin ta'addanci. Hoto: Economic and Financial Crime Commission.
Asali: Facebook

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabun Kaura Namoda da Birnin Magaji, Aminu Sani-Jaji ne hukumar ke zargi.

Kara karanta wannan

Kwara: Sun fadi gaskiya bayan cafke likita da wasu da zargin satar mahaifa da cibiyar jariri

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa ana zargin dan majalisar ne da laifin daukar nauyin ayyukan ta'addanci a jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda suka nemi a hukunta Aminu Jaji

EFCC ta tabbatar da haka ne yayin da wasu matasa 'yan kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa (NPYAC) suka shigar mata da korafi.

Matasan sun gudanar da zanga-zanga ne a hedikwatar hukumar tare da mika bukatar binciken dan majalisar cikin gaggawa,.

Amiu Jaji: Martanin hukumar EFCC

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ne ya karbi matasa masu zanga-zanga hedikwatar hukumar a jiya Juma'a.

Oyewale ya tabbatar wa matasan cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukan mataki kan dan majalisar.

Yaushe EFCC za ta dauki mataki?

Kakakin hukumar ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa zai mika korafinsu ga shugaban hukumar, Olanipekun Olukoyede ba tare da bata lokaci ba.

Kara karanta wannan

MURIC: Kungiyar musulunci ta takalo Ministar da ta hana auren marayu 100 a Neja

Ya kuma kara da cewa hukumar za ta dauki mataki kan dan majalisar cikin kwanaki kadan masu zuwa.

Jawabin mai magana da yawun kungiyar NPYAC

Kakakin kungiyar NPYAC, kwamared Felix Great ya ce suna zargin dan majlisar da tallafawa yan bindiga domin cimma manufa ta siyasa.

Saboda da haka suka mika kukansu ga hukumar EFCC domin daukan matakin da ya kamata a kan dan majalisar, rahoton TVC.

EFCC ta tsare ministan Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa Hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama tsohon ministan Muhammadu Buhari, Hadi Sirika.

EFCC ta kama shi ne bisa zargin sa da hannu cikin badakalar kudi sama da naira biliyan 8 a lokacin da yake ministan jiragen sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel