Tinubu Ya Nada Tsofaffin Gwamnoni 4 da Ministan Buhari a Manyan Muƙamai

Tinubu Ya Nada Tsofaffin Gwamnoni 4 da Ministan Buhari a Manyan Muƙamai

  • Shugaban Bola Tinubu ya nada shugabannin kwamitin gudanarwa da mambobinsu a manyan makarantun Najeriya 111
  • Daga cikin wadanda suka samu mukamin akwai tsofaffin gwamnoni hudu da kuma tsohon Ministan Muhammadu Buhari a Najeriya
  • Hakan ya biyo bayan nadin mutane 555 a kwamitin gudanar da mambobinsu a manyan makarantu 111 a fadin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin shugabanni da mambobi gudanarwa a manyan makarantun Najeriya.

Tinubu ya naɗa akalla 555 a manyan makarantun Najeriya guda 111 da suka haɗa da Jami'o'i da Kwalejin Fasaha da kuma na ilimi.

Tinubu ya ba tsofaffin gwamnoni da Ministan Buhari mukamai a gwamnatinsa
Bola Tinubu ya nada tsofaffin gwamnoni 4 shugabannin kwamitin gudanarwa a Jami'o'in Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Tinubu ya nada mutane 555 a mukamai

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya ba Farfesa Attahiru Jega babban mukami a gwamnatin tarayya

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yau Asabar 18 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya wallafa jerin sunayen wadanda suka samu mukamin har guda 555 daga manyan makarantu 111 a Najeriya.

Daga cikin wadanda suka sani mukamin akwai tsofaffin gwamnonin jihohin Ebonyi da Bauchi da Zamfara da kuma Adamawa.

Tsofaffin gwamnoni da Tinubu yaba mukami

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na Jami'ar Tarayya da ke Jos ajihar Plateau.

Shinkafi zai jagoranci kwamitin da mambobinsu kamar haka Malandi Adamu Sabo da Chijioke Paul Okeifufe da Ayo Afolabi da kuma Mohammed Dharr Abdullahi.

Sai kuma tsohon gwamnan Bauchi, Isa Yuguda da zai jagoranci kwamitin gudanarwa na jami'ar tafi-da gidanka watau 'Open University'.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Soki Shirin Tinubu Na Kashe Naira Tiriliyan 20 da Aka Ajiyewa ‘Yan Fansho

A cikin mambobinsu akwai Betty Efekodah da Bawuro Bapetel da Dakta Gidado Bello Kumo da kuma Bola Akinola.

Tsohon gwamnan Adamawa, Bala Ngilari kuma shi ne zai jagoranci kwamitin a Jami'ar Calabar da ke jihar Cross River.

Karkashinsa akwai mambobi kamar haka, Adebisi Obawale da Idowu Mafimisibe da Nbadiwe Emelnmna da kuma Sadat Garba.

Har ila yau, tsohon gwamnan Ebonyi, Martini Elechi zai jagoranci kwamitin a Jami'ar Tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa.

A cikin kwamitin akwai mambobi kamar haka Imamudden Ahmed da Ismalla Mohammed da Farfesa Seun Liberty da Moses Osogi.

Tinubu ya ba tsohon Ministan Buhari mukami

Sai kuma tsohon Ministan Kasafi da tsare-tsare, Udoma Udo Udoma zai jagoranci kwamitin a Jami'ar Bayero da ke jihar Kano.

Mambobin kwamitin sun hada da Farfesa Idris Nasir Maiduguri da Farfesa Uchenna Newi da Salisu Mohammed Birniwa da kuma Fola Akinsete.

Tinubu ya naɗa Yayale Ahmed a mukami

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Yayale Ahmed mukami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Bayan Yayale Ahmed, Tinubu ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Zamfara, Mahmud Aliyu Shinkafi shugaban kwamitin gudanarwa a Jami'ar Tarayya da ke Jos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.