Mai Dokar Bacci: Mazauna Kano sun Zargi Sojan Sama da Kashe Dan Uwansu

Mai Dokar Bacci: Mazauna Kano sun Zargi Sojan Sama da Kashe Dan Uwansu

  • Wasu mazauna Gwagwarwa a jihar Kano sun yi zanga zanga domin nuna fushinsu bisa kisan da uwansu da ake zargin jami'in sojin sama ya yi
  • Mahaifin marigayin, Shu'aibu Bala ya bayyana cewa bayan dansa ya kammala aikin dare ne Aminu Oga ya kira shi ya yi masa wani aiki
  • Daga bisani Yusuf Shu'aibu ya nemi a bashi kudin abinci, amma Aminu Oga ya rufe shi da duka har da cizon da ya yi ajalinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Mazauna yankin Gwagwarwa da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano sun zargi wani jami'an sojin saman Najeriya da kashe musu dan uwa Yusuf Shu'aibu mai shekaru ashirin da uku.

Kara karanta wannan

JAMB 2024: Lauya ya ja hankalin gwamnati kan hana dalibai masu hijabi rubuta UTME

'Yan uwan marigayin sun zargi wani jami'in sojin saman Najeriya, Oga Aminu da lakadawa marigayin duka, har ya yi masa raunukan da su ka yi sanadiyyar rasuwarsa.

An zargi soja da kashe wani matashi a Kano
Ana zargin wani Sojan Sama, Aminu Oga da kashe wani matashi Yusuf Shu'aibu a Kano Hoto: Aminu Abdullahi Ibrahim
Asali: UGC

Marigayi Yusuf Shu'aibu na aikin goge-goge a asibitin sojin saman kasar nan, inda a nan ne ya san Oga Aminu da ake zargi da kashe shi, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An gartsawa 'da na cizo," Mahaifin Yusuf

Mahaifin marigayi Yusuf, Shu'aibu Bala cike da takaici ya ce bayan 'dansa ya kammala aikin dare ne Oga Aminu ya ba shi wani aiki.

A cewar uban cike da bakin ciki, bayan Yusuf ya kammala aikin ne sai ya nemi a ba shi kudin sayen abinci.

Maimakon haka ne aka rufe shi da duka, har da alamun cizo a jikinsa, inda ya nemi hukumomi da gwamna Abba Kabir Yusuf su taimaka wajen bi masa hakkinsa.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

A martanin da rundunar sojin saman kasar nan ta yi ta bakin kakakinta, Air Vice Marshal Edward Gabwet, dama marigayin ya taba samun hatsaniya da wani kafin yanzu, amma ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin rasuwarsa, kamar yadda Sahara reporters ta wallafa.

Soja ya yi ajalin wani a Delta

A baya mun ruwaito muku cewa wani jami'in soja ya harbe wani matashi a jihar Delta, an yi harbin ne daidai lokacin da gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa ya sanya dokar hana zirga-zirga.

Duk da ta tabbatar da faruwar harbin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Onome Onovwakpoyeya, ta ce ba su da cikakken bayani kan lamarin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel