JAMB 2024: Lauya Ya Ja Hankalin Gwamnati Kan Hana Dalibai Masu Hijabi Rubuta UTME

JAMB 2024: Lauya Ya Ja Hankalin Gwamnati Kan Hana Dalibai Masu Hijabi Rubuta UTME

  • Wasu jami'ai a cibiyoyin jarrabawar JAMB a Najeriya kan kasance masu nuna rashin adalci da wariya ga mata Musulmai masu sanye da hijabi a wasu jihohin
  • A kwanakin baya ne hukumar ta JAMB ta bayyana fushinta kan yadda wani lamari ya auku, inda aka tursasa Musulma ta cire hijabi kafin shiga jarrabawar UTME a Legas
  • A wata hira da Legit.ng ta yi da wani babban lauya a Najeriya, Yusuf Nurudeen, ya koka da yadda ake cin zarafin 'yan mata Musulmi ba tare da aikata wani laifin da ya sabawa kasa ba

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Ikoyi, jihar LegasWani lauya mazaunin Legas, Yusuf Nurudeen, ya shaidawa al’umma cewa, duk wanda ya musgunawa ‘yan mata Musulmai masu sanya hijabi a Najeriya to tabbas sun aikata babban laifin ta’addanci, kuma za a iya daukar mataki a kansu.

Kara karanta wannan

A tuna da matattu: Sanata a Kano ya rabawa 'yan mazabarsa likkafani da tukwanen kasa

Nurudeen, wanda shi ne mu’assasin gidauniyar kare muradu da ci gaban jama’a, a wata hira da Legit, ya yi nuni da sashe na 38 na kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, wanda ya bai wa kowane dan Najeriya ‘yancin aiwatar da addini daidai fahimtarsa.

An hana dalibai masu hijabi rubuta UTME a Legas
Lauya ya yi martani kan hana wasu rubuta UTME a Legas | Hoto: Juan Monino, Prof Is'haq O. Oloyede
Asali: UGC

Ya ba da shawarar a dauki matakin hukunta masu musgunawa Musulmai mata masu hijabi, inda yace hakan ya kamata ya shafi jami’an da ke musgunawa mata a lokutan jarrabawar JAMB, WAEC, ko NECO.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da lauya ya hango a lamarin

Nurudeen ya shaidawa wakilin Legit cewa:

"Yanzu abin na zama laifi. Kundin Tsarin Mulki ya haramta nuna wariyar addini."

Ya ci gaba da cewa:

“Ina ganin ya kamata majalisarmu ta daukaka lamarin zuwa matakin da za ta maida hakan ya zama laifin ta’addanci idan aka nunawa wani bambanci domin a hukunta mutane.

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

"Bai kamata a tilasta maka abin da baka so ba, ko burinka ba, ko alakarka ta addini ba, ko dai ka sanya ko kuma kadaaku suturta da wani salon tufafi. Don haka, ýanci ne na tushe."

Har ila yau, Barr. Nurudeen ya shawarci JAMB da ta janye lasisin duk wata cibiya da aka samu tana nuna bambanci da wariyar addini.

Karin labarai game da JAMB 2024:

Daliban Islamiyya sun yiwa UTME cin kaca

A wani labarin kuma, Legit ta tattauna da wata makarantar Islamiyyar da ta horar da daliban da suka ci UTME da kyau.

An gano yadda daliban suka samu maki mai kyau a jarrabawar da aka gudanar makwanni kadan da suka gabata.

'Yan Najeriya da dama ne suka yada sakamakon jarrabawarsu, inda aka ci jarrabawar daga 200 zuwa 300 da 'yan kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.