Wahalar Fetur: Dillalan Mai Sun Yi Barazanar Janye Ayyukansu Saboda ‘Kudin Fito’

Wahalar Fetur: Dillalan Mai Sun Yi Barazanar Janye Ayyukansu Saboda ‘Kudin Fito’

  • Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta yi barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar wanda zai iya gurgunta harkar man fetur
  • Oliver Okolo, shugaban kungiyar reshen Aba wanda ya bayyana hakan ya ce IPMAN na dab da daukar wannan matakin
  • IPMAN, ta ce za ta dauki matakin ne sakamakon rashin biyanta sama da N200bn na 'kudin fito' da take bin hukumar NMDPRA

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kungiyar dillalan mai ta kasa IPMAN ta ce za ta janye ayyukanta ta hanyar rufe gidajen manta wanda hakan zai iya gurgunta harkar man fetur a fadin Najeriya.

Kungiyar IPMAN ta yi barazanar shiga yajin aiki
Dillalan mai sun yi barazanar rufe gidajen mai a fadin Najeriya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

IPMAN na bin bashin kudin fito

Kungiyar IPMAN, ta ce za ta dauki matakin ne sakamakon rashin biyanta sama da Naira biliyan 200 na 'kudin fiton' man fetur, rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPCL ya dauki matakin kawo karshen dogon layin da ke gidajen mai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ci gaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin man fetur, lamarin da ya janyo hauhawar farashin kayayyaki.

'Kudin fito' kudi ne da ake biya na jigilar fetur daga ma'ajiyar man zuwa yankunan da aka amince a rarraba shi domin tabbatar da daidaiton farashinsa a duk faɗin ƙasar.

"NMDPRA take rike da kudin" - IPMAN

Oliver Okolo, shugaba kuma mai magana da yawun kungiyar reshen Aba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar bayan wani taron manema labarai a ranar Talata.

Jaridar The Cable ta ruwaito Okolo ya ce hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Najeriya (NMDRA) ce ta rike kudaden da ake magana akai.

Okolo ya ce NMDPRA ta gaza biyan bashin Naira biliyan 200, wanda ya taru tun Satumba 2022 duk da umarnin biyan daga Heineken Lokpobiri, ministan albarkatun man fetur.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPCL ya fadi ranar da matatar man Kaduna za ta dawo bakin aiki

Halin da dillalan fetur suka shiga

Ya ce jinkirin da NMDPRA ta yi na biyan bashin ya haifar da "mutuwar da yawa daga cikin mambobinmu da kuma durkushewar kasuwancinsu".

“A matsayinmu na ‘yan kasuwa, mambobinmu sun samu lamuni na banki domin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na sayar da mai a cikin lunguna da sako na Najeriya.
“Sai dai abin takaici ne sanin cewa da yawa daga cikin mambobinmu sun fada fatara, kasuwancinsu ya durkushe sakamakon gazawar NMDPRA na biyansu hakkinsu wanda zai basu damar biyan bankuna bashin da suka karba."

-A cewar Okolo.

"Lokacin da fetur zai wadata" - IPMAN

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya ta ce nan da makonni biyu man fetur zai wadata a lungu da sako na kasar.

Kungiyar IPMAN ta bayyana hakan ne a yayin da kasar ke fama da karancin man tana mai cewa kamfanin NNPCL ya basu tabbacin samun mai zuwa lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel