Wahalar Fetur: NNPCL Ya Dauki Matakin Kawo Karshen Dogon Layin da ke Gidajen Mai

Wahalar Fetur: NNPCL Ya Dauki Matakin Kawo Karshen Dogon Layin da ke Gidajen Mai

  • Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce a halin yanzu yana da sama da lita biliyan 1.5 na man fetur wanda zai rabawa 'yan kasuwa
  • Babban jami’in sadarwa na NNPC, Olufemi Soneye wanda ya bayyana hakan ya ce nan da zuwa ranar Laraba za a daina wahalar man
  • Kungiyar dillalan man fetur (lPMAN) ta ce fetur ba zai samu a Abuja da wuri ba saboda nisan birnin da Legas da rashin hanya mai kyau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Legas - Kamfanin man fetur na Najeriya ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a kawo karshen karancin man fetur da dogayen layukan da ake fama da su a zuwa Laraba.

Kara karanta wannan

Wahalar fetur: NNPCL ya fadi ranar da matatar man Kaduna za ta dawo bakin aiki

Kamfanin NNPCL ya yi magana kan wahalar fetur a Najeriya
NNPCL ya ba da tabbacin cewa zuwa ranar Laraba man fetur zai wadata a Najeriya. Hoto: @nnpclimited
Asali: Getty Images

Babban jami’in sadarwa na NNPC, Olufemi Soneye ne ya bayyana hakan a wani sakon kar-ta-kwana da ya aikatawa jaridar Leadership a ranar Talata a Legas.

NNPCL na da isasshen fetur a kasa

A cewar Mista Soneye, kamfanin a halin yanzu yana da man fetur da ya wuce lita biliyan 1.5 a kasa, wanda zai iya daukar akalla kwanaki 30 kafin ya kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abin takaici, mun samu cikas na tsawon kwanaki uku wajen rabon man, wanda kuma tun a lokacin aka shawo kan matsalar.
"Wasu mutane suna amfani da wannan damar wajen kara kudin fetur din. Duk da hakan, ina da tabbacin zuwa gobe (Laraba) fetur zai wadata a ko ina."

- A cewar Mista Soneye.

Dillalan man fetur sun yi martani

Hakazalika, mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur ta kasa (lPMAN), ya bayyana fatan ganin an samu saukin layukan da ake yi a Legas da Ogun a wannan mako.

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

Jaridar Premium Times ta ruwaito Mista Fashola ya bayyana cewa za a iya samun karin layin masu sayen mai a Abuja saboda nisan kawo man daga Legas.

“Zai iya daukar lokaci kafin a samu saukin wahalar fetur din a Abuja, idan aka yi la’akari da nisan Abuja daga Legas da kuma rashin hanya mai kyau."

- Olufemi Soneye

Matatar man Kaduna za ta dawo aiki

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ba da tabbacin cewa zuwa watan Disambar wannan shekarar matatar man Kaduna za ta dawo aiki.

NNPCL ya yi nuni da cewa matatar za ta iya fara tace ganga 66,000 na man fetur idan ta dawo aiki a watan Disamba yayin da za a kammala dukkanin gyaran a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel