Kudin Shigo da Man Fetur Ya Tashi, Farashin Lita Ya Zarce N1, 200 Yau a Najeriya

Kudin Shigo da Man Fetur Ya Tashi, Farashin Lita Ya Zarce N1, 200 Yau a Najeriya

  • Tashin da Dalar Amurka take yi a kasar nan ta taimaka wajen kara tsadar man fetur da aka dogara da shi a Najeriya
  • Abin da ake zargin ana kashewa kafin litar fetur ta tsallako teku zuwa kasar nan ta rufe N1, 000 lissafin kudin canji
  • Bayan daidaita kudin kasashen waje, babu bambancin farashin Dala wajen shigo da fetur da wajen yin wasu bukatun

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

FCT, Abuja - Mummunan faduwar da Naira take yi a kasuwar canji, ya jawo hakikanin farashin man fetur ya kara tsada a Najeriya.

A ranar Asabar, Leadership ta kawo labari cewa farashin da litar man fetur yake shigowa kasar nan daga kasar waje ya zarce N1, 000.

Kara karanta wannan

NNPCL ya faɗi lokacin da zai kawo ƙarshen wahalar man fetur a Najeriya

Man fetur
Watakila kudin man fetur ya zarce N1000 a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gwamnati ta jawo fetur ya tashi

Sakin farashin Dala a hannun ‘yan kasuwa ya jawo fetur ya kara tashi bayan gwamnatin tarayya ta janye tsarin biyan tallafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan aka yi lissafin Dala a N1, 500, to litar kowane man fetur za ta shigo Najeriya ne a kan N1, 009 a maimakon N720 da yake a Oktoba.

Watanni hudu da suka wuce da Naira ta fi haka daraja, a N720 aka shigo da mai. Duk da haka a lokacin an saida lita kan kusan N700.

Bayan kudin da aka shigo da man daga ketare, za a biya kudin dako da na dauka daga tashoshin NNPCL zuwa gidajen mai a kasar.

Babu tabbacin fetur ya wuce N1000

Shugaban kungiyar PETROAN ta masu sarin kayan mai a Najeriya, Billy Gillis-Harry yana da ja game da farashin litar da ake tunani.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Mista Billy Gillis-Harry ya ce akwai abubuwan da ake la’akari da su a kudin fetur, daga ciki akwai inshora, kudin ganguna da haraji.

An rahoto cewa gwamnatin Najeria tana kashe N907.5bn a matsayin tallafin fetur duk da Bola Tinubu ya sanar da yin watsi da tsarin.

Business Day ta fitar da rahoton da ya karfafa zancen tashin da fetur ya yi a kasar.

Idan hakan ta tabbata, IMF tayi gaskiya da ta zargi gwamnati da saukakawa talaka kudin fetur domin ganin farashi bai tashi ba.

Za a binciki bashin da Najeriya ta ci

Kuna da labari cewa an kafa kwamiti mai karfi a majalisar dattawa da zai binciki bashin N30tr da gwamnatin baya ta karbo a Najeriya.

A lokacin Muhammadu Buhari, Godwin Emefiele ya yi ta buga kudi domin a ba gwamnatin tarayya aro wanda ya damalmala kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel