Wahalar Fetur: NNPCL Ya Fadi Ranar da Matatar Man Kaduna Za Ta Dawo Bakin Aiki

Wahalar Fetur: NNPCL Ya Fadi Ranar da Matatar Man Kaduna Za Ta Dawo Bakin Aiki

  • Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce za a kammala aikin gyaran matatar man Kaduna (KRPC) a watan Disamba, 2024
  • Shugaban KRPC, Mustafa Sugungun wanda ya bayyana hakan ya ce matatar za ta fara da tace gangunan mai 66,000 idan ta dawo bakin aiki
  • Wannan dai na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na ganin dukkanin matatun kasar sun dawo aiki domin magance karancin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya ce za a kammala aikin gyaran matatar mai ta Kaduna (KRPC) a watan Disamba na wannan shekara.

Matatar man da ta daina aiki na tsawon shekaru saboda rashin kulawa, za ta fara da kashi 60 idan ta dawo da aiki, Radio Nigeria ya ruwaito.

Kara karanta wannan

Hukumar kwallon kafar Najeriya ta nada sabon kocin tawagar Super Eagles

NNPCL ya yi magana kan kammala gyara matatar mai ta jihar Kaduna
Kamfanin NNPCL ya ce zuwa watan Disamba, 2024 matatar mai ta Kaduna za ta dawo aiki. Hoto: @nnpclimited
Asali: UGC

Mambobin kwamitin majalisar dattijai kan harkokin man fetur a kasa karkashin jagorancin Sanata Ifeanyi Ubah sun kai ziyarar sa ido a matatar man a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Watan da matatar za ta dawo aiki

A yayin ziyarar babban daraktan KRPC, Mustafa Sugungun ya shaidawa kwamitin cewa matatar wacce ke tace ganga 110,000 a rana za ta fara da tace ganga 66,000 a Disamba.

Channels TV ta ruwaito shugaban na KRPC ya ce ana aikin gyara, wanda a halin yanzu ya kai kashi 40, ana sa ran kammala shi cikin wa'adin da aka diba.

“A halin yanzu, muna kan hanyar cimma kashi 40 na gyaran da muke. Muna da yakinin za mu dawo da aikin matatar na aƙalla kashi 60 zuwa 31 ga watan Disamba, 2024.
“Matatar mai ta Kaduna na da karfin tace ganguna 110,000 ne a kowace rana, amma muna fatan farawa da kashi 60 ne kawai."

Kara karanta wannan

Dillalan mai sun fadi lokacin da wahalar fetur da ta mamaye Najeriya za ta kare

- Mustafa Sugungun.

Gwamnati na kokarin farfado da matatu

A nasa bangaren, Sanata Ubah ya bayyana cewa ziyarar gani da idon na daga cikin kokarin hadin gwiwa na shugaba Bola Tinubu da majalisar dokokin kasar.

Sanata Ubah, ya ce burin gwamnati shi ne tabbatar da cewa dukkanin matatun man kasar nan sun dawo bakin aiki domin kawo karshen wahalar fetur da shigo da man daga kasashen waje.

Matatar man Dangote ta karya farashi

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa matatar man Dangote ta kara karya farashin man dizal da na jiragen sama zuwa N940 da N980 a kan kowacce lita.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake murnar matatar ta rage farashin dizal zuwa N1,000 a makonnin da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel