Dillalan Mai Sun Fadi Lokacin da Wahalar Fetur da Ta Mamaye Najeriya Za Ta Kare

Dillalan Mai Sun Fadi Lokacin da Wahalar Fetur da Ta Mamaye Najeriya Za Ta Kare

  • A yayin da karancin man fetur ya fara kamari a jihohin Najeriya, dillalan mai na Najeriya sun ce nan da makonni biyu komai zai daidaita
  • Kungiyar IPMAN ta ce kamfanin NNPCL bai iya wadatar da 'yan kasuwa da man ba wanda ya kawo karancinsa a gidajen mai na kasar
  • Sai dai kakakin kungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce NNPCL ya ba su tabbacin cewa jiragen mai na dab da shigowa kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN), ta bayyana cewa za a dauki akalla makonni biyu kafin a daina wahalar man fetur da ake fama da ita a wasu jihohi yanzu.

Kara karanta wannan

Dillalan fetur sun zargi kamfanin NNPCL da hana su mai

Kungiyar IPMAN ta yi magana kan wahalar man fetur da ake fuskanta a Najeriya
IPMAN ta ce za a dauki akalla makonni biyu kafin a daina wahalar man fetur a Najeriya. Hoto Getty Images
Asali: Getty Images

Wannan na zuwa yayin da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya dage a jiya kan cewa yana da isasshen man fetur a kasa wanda zai wadaci kasar baki daya.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na kungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike, ya ce babu man fetur a hannun 'yan kasuwa a halin yanzu, rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya dillalan man fetur a yanzu na fuskantar kalubale wajen nemo man saboda galibin matatun mai a Turai sun tafi hutun gyararraki da sukanyi lokaci zuwa lokaci.

Me ya jawo karancin fetur a Najeriya?

Ukadike ya kuma dora alhakin karancin fetur da ake samu a kan matsalolin shigo da man da kuma tafiyar hawainiyar sabunta lasisin ‘yan kasuwa da hukumar NMDPRA ke yi.

Jaridar The Guardian ta ruwaito shi yana cewa ‘yan kasuwa 1,050 ne kawai daga cikin 15,000 da NMDPRA ta sabunta lasisinsu.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur ta jawo tashin farashin motoci da sauran abubuwan hawa

"Da zarar an samu tsaiko wajen shigo da man ko kuma rashin wadatuwarsa, shi ne za a fara ganin gidajen mai na rufewa, ko kuma a kara kudi, wanda zai jawo layin masu sayen man.
"A bangaren kamfanin na NNPCL, wanda shi ne kadai ke samar da man fetur a Najeriya, ya alakanta kalubalen da ya samu ga matsalolin sufurin man."

- Chinedu Ukadike.

Halin da ake ciki yanzu

Jami’in hulda da jama’a na IPMAN ya ce shugaban rukunin kamfanin na NNPCL ya ba su tabbacin cewa jiragen ruwa dauke da fetur na dab da karasowa Najeriya.

Ukadike ya ce:

"Muna sa ran nan da mako daya ko biyu masu zuwa kamfanin NNPCL zai samar da wadataccen mai ga 'yan kasuwa wanda hakan zai sa komai ya dawo kamar yadda aka saba”.

An kara kudin motocin haya

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa karancin man fetur da ake fama da shi yanzu a kasar ya jawo an kara kudin motocin haya da sauran ababen hawa a Najeriya.

Mutane da dama sun bayyana yadda suka shiga damuwa sakamakon karin kudin ababen hawan yayin da wasu suka koma tafiya da kafa sakamakon nunkawar kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel