'Yan bindiga Sun Kai Ƙazamin Farmaki Kan Bayin Allah a Watan Azumi, Sun Kashe Mutane da Yawa

'Yan bindiga Sun Kai Ƙazamin Farmaki Kan Bayin Allah a Watan Azumi, Sun Kashe Mutane da Yawa

  • Wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun farmaki kauyen Agojeju-Odo da ke jihar Kogi, sun halaka mutane da yawa kuma sun ƙona gidaje
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce CP ya tura karin jami'an ƴan sanda
  • Wani shugaban al'umma a yankin wanda ya nemi a sakaya bayanansa ya ce maharan sun buɗe masu wuta ne ba zato ba tsammani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai kazamin farmaki a kauyen Agojeju-Odo da ke yankin ƙaramar hukumar Omala a jihar Kogi.

Maharan ɗauke da mugayen makamai sun buɗe wa mutanen kauyen wuta, kana suka ƙona gidaje da dama a harin na yau Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke matasa masu yunkurin kona sansanin 'yan gudun hijira a jihar Arewa

Yan sandan Najeriya.
Ana fargabar yan bindiga sun kashe mutane a kauyen jihar Kogi Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

A wata hira ta wayar tarho, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar sabon harin ga wakilin jaridar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Ya kuma ƙara da cewa tuni kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Bethrand Onuoha, ya tura ƙarin dakarun ƴan sanda na sashin dabaru zuwa yankin tare da wasu jami'an tsaro.

Aya ya ce:

"Eh tabbas an kai sabon hari kan wani kauye a karamar hukumar Omala. CP ya tura ƙarin dakarun ƴan sanda tare da wasu hukumomin tsaro."

Aya ya ƙara da cewa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin harin da kuma gano wadanda ke da hannu a kai wannan harin.

Yadda maharan suka yi ɓarna

Wani shugaban al'umma a yankin wanda ya sha da ƙyar, ya ce maharan sun shiga garin ne ba zato ba tsammani, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja, sun tafka mummunar ɓarna a watan azumi

Ya shaidawa jaridar Daily Post cewa zuwa yanzun an gano gawar mutane 27, yayin da ƴan banga suka fantsama cikin jeji domin nemo waɗanda suka ɓata.

Ya bayyana cewa makonni uku da suka shige an yi ta yaɗa jita-jitar cewa da yiwuwar ƴan bindiga su kawo hari kauyen.

A cewarsa, sakamakon haka ne aka sanar da sabon shugaban ƙaramar hukuma na riƙo, Mark Edibo, wanda ya tabbatarwa mazauna yankin cewa za a ba su tsaro.

Ƴan bindiga sun kara shiga Abuja

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi garkuwa da wasu biyu a yankin ƙaramar hukumar Bwari da ke birnin tarayya Abuja.

Wata majiya a rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa jami'ai sun matsa ƙaimi da nufin kamo maharan duk inda suka shiga suka ɓuya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262