'Yan Bindiga Sun Ƙara Shiga Abuja, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Watan Azumi

'Yan Bindiga Sun Ƙara Shiga Abuja, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Watan Azumi

  • Yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun yi garkuwa da wasu biyu a yankin ƙaramar hukumar Bwari da ke birnin tarayya Abuja
  • Wata majiya a rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa jami'ai sun matsa ƙaimi da nufin kamo maharan duk inda suka shiga suka ɓuya
  • Duk wani ƙoƙari na jin ta bakin rundunar ƴan sanda bai cimma nasara ba amma wani jami'in gwamnati ya tabbatar da fauwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Gaba da ke yankin ƙaramar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja.

Bisa ga binciken da aka yi, ‘yan bindigar da yawansu ya haura shida, sun shiga kauyen ne da misalin karfe 12:15 na tsakar dare wayewar garin Laraba.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi kazamin artabu da ƴan bindiga, mutane da yawa sun mutu

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga sun kara shiga yankin Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Maharan sun halaka mutum ɗaya yayin harin, kuma suka yi awon gaba da wasu mutum biyu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani jami’in gwamnati, wanda ke zaune a unguwar ya shaida wa ƴan jarida cewa an yi garkuwa da mutum biyu sannan aka kashe daya a harin.

Yadda lamarin ya faru

Wata majiya mai karfi a cikin rundunar ‘yan sanda, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce dakarun ‘yan sanda na nan suna farautar ‘yan bindigan da suka kai harin.

Ya koka game da ƙaruwar masu kai wa ƴan bindiga bayanan sirri, yana mai ƙara wa da cewa matsalar infomomi babban abin damuwa ce.

Majiya daga cikin jami'an tsaron ta ce akwai masu ba ƴan bindiga bayanan sirri a cikin al'umma kuma ana bukatar ta shi tsaye haiƙan domin magance su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanya mutane farin ciki awanni 24 bayan sace kananan yara 30 a Arewa

Gaba, shi ne kauyen da shugaban ƙaramar hukumar Bwari na yanzu, John Gabaya ya fito.

Duk kokarin jin ta bakin jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh ya ci tura dominba ta ɗaga kira ko amsa sakonnin da aka tura mata ba.

'Yan bindiga sun tarwatsa garuruwa 551

A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun raba mutane sama da 200,000 da muhallansu a yankunanan kananan hukumomi 12 na jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna karkashin Malam Uba Sani ta ce mutane 289,375 ne suka gudu suka bar gidaje a garuruwa 551 saboda matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel