Ana Tsaka da Shan Ruwa, 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, Sun Sace Malamin Musulunci a Arewa

Ana Tsaka da Shan Ruwa, 'Yan Bindiga Sun Kai Hari, Sun Sace Malamin Musulunci a Arewa

  • Miyagu sun sake kai hari yankin Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi inda suka sace malamin Musulunci, Quasim Musa
  • Maharan sun yi garkuwa da babban limamin garin Iyara da ke jihar bayan sun yi ta harbe-harbe domin firgita mutanen yankin
  • Lamarin ya faru ne bayan shan ruwa a daren jiya Litinin 25 ga watan Maris kamar yadda rundunar 'yan sanda ta tabbatar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Wasu 'yan bindiga sun sace fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya.

Maharan sun sace babban limamin ne na Iyara da ke karamar hukumar Ijumu a jihar mai suna Sheikh Quasim Musa.

Kara karanta wannan

Kano: Daina amfani da soshiyal midiya da wasu sharuɗa da kotu ta kafawa Murja Kunya

Yan bindiga sun yi garkuwa da malamin Musulunci a Arewa
Maharan sun sace Sheikh Quasim Musa a gidansa da ke jihar Kogi. Hoto: Quasim Musa.
Asali: Facebook

Yaushe aka sace malamin Musuluncin Kogi?

Tribune ta tattaro cewa an sace Musa ne da daren jiya Litinin 25 ga watan Maris a garin Ilukpa da ke karamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga yankin ta ce maharan sun birkita mutanen garin da harbe-harbe kafin su dauke malamin su tafi da shi.

Wani daga cikin iyalan malamin da ya bukaci a boye sunansa ya ce har zuwa yanzu ba su samu bayani daga maharan ba.

Majiyar ta ce:

"Ya ku 'yan yankin Iyara, rashin tsaro da ke samun kasar ya shafe mu a wannan yanki namu."
"A ranar 25 ga watan Maris, wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun sace babban limamin Iyara, Sheikh Quasim Musa bayan harbe-harbe."

Al'ummar Kogi sun roki addu'a daga jama'a

Har ila yau, majiyar ta yi Allah wadai da harin musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan hari a Yobe, sun hallaka soja

Ta bukaci jama'an yankin da su dage da addu'a domin ganin an ceto malamin daga hannun miyagun.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Talata 26 ga watan Maris.

Maharan sun farmaki dakunan daliban Jami'a

Kun ji cewa wasu mahara sun kai hari dakunan kwanan dalibai mata a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Lokaja a jihar Kogi.

Maharan sun raunata dalibai guda biyu tare da sace musu wayoyi da kudi da sarki yayin harin da suka shafe awa biyu su na yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel