Kaduna: An Ceto Daliban Makaranta 137 da ‘Yan Bindiga Suka Dauke Bayan Kwana 16

Kaduna: An Ceto Daliban Makaranta 137 da ‘Yan Bindiga Suka Dauke Bayan Kwana 16

  • Daliban makarantar Kuriga da aka yi garkuwa da su sun kubuta kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da sanarwa
  • Gwamna Uba Sani ya shaida haka a safiyar Lahadi, sai dai bai yi cikakken bayanin yadda ‘yan makarantar suka tsira ba
  • Jawabin Mai girma cike yake da yabon Bola Tinubu da Nuhu Ribadu yayin da yaran suka tsira daga hannun ‘yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Daliban Kuriga sun bar hannun 'yan bindiga

KadunaDaliban makarantar Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna sun shaki iskar ‘yanci.

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wadannan yara sun fito da su kamar yadda hukuma ta tabbatar a yau Lahadi.

Uba Sani
Gwamna Uba Sani ya ce sojoji sun ceto daliban Kuriga a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

N6bn: 'Yan APC a Kano sun taso Gwamna Abba a gaba kan kudaden ciyar da bayin Allah a Ramadana

Uba Sani ya sanar da ceto yaran Kuriga

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ba da wannan sanarwa a shafukansa na sadarwa da safiyar nan.

Malam Uba Sani a jawabin da ya fitar a shafin Facebook, ya fara da sunan wa Allah SWT wajen sanar da nasarar.

Mai girma gwamna ya yi wa Bola Ahmed Tinubu, GCFR godiya ganin yadda ya ba da fifiko wajen ganin an ceto yaran.

Gwamna Uba Sani ya ce Mai girma shugaban kasa ya yi tsayin-daka wajen ganin an ceto yaran babu ko da kwarzane.

Kuriga: Bangaren jawabin Gwamnan Kaduna

"A lokacin da yaran suke tsare, na yi magana da Shugaban kasa sau da-dama.
(Tinubu) ya taya mu takaici, ya taya mu jaje kuma ya yi aiki dare da rana domin ganin daliban sun dawo."

- Uba Sani

Kara karanta wannan

Mun tada matattu sama da 50 a cocina bayan tabbatar da mutuwarsu, inji malamin coci Chris

Ribadu da Sojoji sun taka rawar gani

Jawabin gwamnan ya kunshi ambato na musamman ga Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu.

Uba Sani ya ce sun shafe darare babu barci tare da Malam Nuhu Ribadu saboda a ga yadda za a ceto ‘yan makarantar.

Har ila yau, Sanata Sani ya ce dole a jinjinawa sojoji da suka nuna rashin tsaro da jajircewa wajen kubutar da yaran.

A karshe gwamnatin Kaduna ta yi godiya ga al’ummar Najeriya da suka dage da addu’a har aka ga rana irin ta yau.

Atiku ya koka kan matsalar tsaro

Ana da labari cewa Alhaji Atiku Abubakar ya yi Allah wadai kan matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar nan a yau.

Jagoran adawar kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya nuna yatsa ga Bola Tinubu bayan kashe mutane a Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel