N6bn: 'Yan APC a Kano Sun Taso Gwamna Abba a Gaba Kan Kudaden Ciyar da Bayin Allah a Ramadana

N6bn: 'Yan APC a Kano Sun Taso Gwamna Abba a Gaba Kan Kudaden Ciyar da Bayin Allah a Ramadana

  • 'Yan APC a jihar Kano na ganin kamar Abba Kabir Yusuf ya kalmashe wasu kudade na ciyar da bayin Allah a Ramadana
  • Sun nemi ya ba da bahasin abin da ya yi da wasu adadin kudade masu yawa, kamar yadda wani rahoto ya fada
  • Ana ci gaba da ciyar da bayin Allah a watan Ramadana a Kano da sunan shirin rage radadi ga talakawan jihar

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Kano - Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano ta taso gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan batun da ya shafi ciyarwar Ramadana.

A rahoton da muka samo, an ce sun nemi gwamnan da ya yi cikakken bayani kan yadda ya kashe Naira biliyan 6 da aka ware domin ciyar da bayin Allah a watan Ramadan a jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Da yake jawabi yayin kaddamar da rabon kayan abincin ga 'yan jam'iyyar a karamar hukumar Dawkin Tofa a ranar Asabar, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, ya ce akwai bukatar bahasi kan kudin, rahoton Daily Trust.

Ana zargin Abba da yin kwana da kudin Ramadana
APC ta nemi Abba ya ba da bahasin kashe kudin Ramadana | Hoto: @kyusufabba, @apcnigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin ba da tallafin azumi a Kano

Ya ce sun yanke shawarar kawo dauki ga magoya bayansu da sauran ‘yan asalin jihar ne domin rage musu radadin tattalin arziki.

Daily Post ta naqalto Abdullahi Abbas yana cewa:

“Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Umar Ganduje, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, da shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar Bichi, da sauran jama’a, ciki har da ni, sun ba da gudummawar kudi domin sayen shinkafa don rabawa ga ‘yan jam'iyya."

Ya zuwa yanzu dai ba a ga maciji tsakanin 'yan APC da jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano tun bayan kammala shari'ar da ta ba Abba gsakiyar ci gaba da mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai mummunan farmaki Zamfara, sun halaka masu azumi da dama

Dangote ya kaddamar rabon abinci a Najeriya

A wani labarin, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya kaddamar da wani shirin rabon buhunan shinkafa miliyan a fadin Najeriya.

Dangote ya fara rabon ne da buhunan farko guda 120,000 a jihar Kano, cewar rahotonnin da muke samu.

Rabon kayan abincin wanda za a kashe Naira biliyan 15, an fara shi ne a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, a Kano saboda yawanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel