Mun Tada Matattu Sama da 50 a Cocina Bayan Tabbatar da Mutuwarsu, Inji Malamin Coci Chris

Mun Tada Matattu Sama da 50 a Cocina Bayan Tabbatar da Mutuwarsu, Inji Malamin Coci Chris

  • Malamin addinin Kirista ya bayyana yadda yake tada matattu a cocinsa, ya tada sama da 50 a cikin shekara
  • Wannan lamari ya jawo cece-kuce, inda wasu ke ganin hakan ba lamari ne mai saukin faruwa ba ga danadam
  • Ba sabon abu bane malaman addinin Kirista su yi da'awar tada matattu a cocinsu, musamman a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya - Babban malamin Cocin Christ Embassy, Chris Oyakhilome, ya tada kura bayan kalaman da ya yi a baya-bayan nan, lamarin da ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

A yayin wata addu'ar waraka da ya yi na kwanaki uku a kafar LoveWorld USA, faston mai shekaru 60 ya tabbatar da cewa cocinsa dawo da matattu sama da 50.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu ta gurfanar da shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bodejo

Wannan lamari mai ban mamaki dai ya faru ne daga ranar 15 zuwa 17 ga Maris, 2024, inda ya ja hankali da muhawara a duniya.

Malamin coci ya yi ikrarin tada matattu a duniya
Mun tada matattu sama da 50, inji fasto Chris | Hoto: Pastor Chris
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanne irin mutane aka tayar daga mutuwa?

A bidiyon kai tsaye da aka yada a shafin Facebook na LoveWorld USA a ranar 17 ga Maris, fasto Oyakhilome ya bayyana cewa aikinsa na 'tashin matattu' ya kunshi tado da mutane daban-daban masu shekaru daban-daban.

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, ya ce:

“A cikin shekarar da ta gabata, mun sami sama da mutane 50 da muka yarar daga mutuwa, sama da mutane 50.
“Ta yaya za ka ba da bayanin irin wadannan abubuwan? Manya da matasa, a kasashe daban-daban, ta yaya za ka yi bayani?"

Wasu za su yi shakkun lamarin

Sai dai, da kansa ya fadi cikin wasa cewa, akwai yiwuwar a yada kokonta da shakku kan wannan batu da ya yi na tada matattu.

Kara karanta wannan

Ana sa ran naira za ta mike, CBN ya biya bashin Dala biliyan 7 da Emefiele ya bari

Ba wannan ne karon farko da ake samun malamin addinin Kirista ya yi da'awar tada matattu ba, an sha yin hakan a kasar nan.

Duk da haka, ana samun masu sharhi da nuna shakku kan lamarin, inda wasu ke ganin malaman na shirga karya ne kawai.

An kama mai ikrarin tada matattu a Najeriya

A wani labarin, an kame wani fasto da ke ikrarin yana tada matattu, inda ake neman ya bayyana dalilai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, faston mai suna Onyeze Jesus ya saki wani bidiyo yana ikrarin zai tada mutanen da suka mutu.

Irin wannan lamari ya zama ruwan dare a tsakanin malaman Kirista a Najeriya, hakan na jawo cece-kuce da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel