Sojoji Sun Rage Mugun Iri Bayan Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda

Sojoji Sun Rage Mugun Iri Bayan Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda

  • Ƴan ta'adda sun kwashi kashinsu a hannu bayan dakarun sojoji sun kai musu farmaki a jihohin Kaduna da Katsina
  • Sojojin sun halaka ƴan ta'adda huɗu a samamen da suka kai musu a maɓoyarsu da ke a jihohin guda biyu
  • Hakan na ƙunshe ne dai a cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriya ya fitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan ta'adda huɗu a wani samame da suka kai a jihohin Kaduna da Katsina.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sojoji sun halaka 'yan ta'adda
Sojoji sun sheke 'yan ta'adda a Kaduna da Katsina Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Nwachukwu ya kuma bayyana cewa sojojin sun kuma daƙile yunƙurin yin garkuwa da wani shugaban makarantar firamare a jihar Filato.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kona wani dan banga kurmus a wani sabon hari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, sojoji sun yi wa ƴan ta'addan kwanton ɓauna a hanyar Gwamtu-Duduwa-Kujeni cikin ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Sojoji sun yi wa ƴan ta'adda kwanton ɓauna

A yayin kwanton ɓaunan, sojojin sun halaka ƴan ta'adda mutum biyu waɗanda ke amfani da hanyar domin kai kayayyaki zuwa dajin Rijana.

Sanarwar ta ƙara da cewa a wani samamen, sojojin bayan sun samu bayanan sirri, sun farmaki maɓoyar ƴan ta'adda a Dutsen Kura cikin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.

A yayin samamen sojojin sun halaka ƴan ta'adda biyu bayan sun yi musayar wuta.

Sanarwar ta ci gaba da cewa dakarun sojojin bayan sun samu kiran gaggawa, sun kuma daƙile yunƙurin yin garkuwa da wani mutum mai suna, Mista Solomon Zakka, wanda shi ne shugaban wata makarantar firamare a Daffo.

An dai sace Mista Zakka ne a gidansa da ke ƙauyen Maiduna cikin ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato.

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun halaka sojoji 22 a wani mummunan kwanton bauna

Sojoji sun sheƙe ƴan ta'addan IPOB

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun sheƙe ƴan ta'addan ƙungiyar IPOB a wani samame da suka kai a jihar Imo.

Sojojin sun halaka ƴan ta'addan ne mutum biyar a ƙauyen Ejemekuru da ke ƙaramar hukumar Oguta ta jihar, bayan sun yi musayar wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel