Ali Nuhu Ya Karɓi Ragamar Hukumar NFC, Ya Kama Aiki Gadan-Gadan a Muƙamin da Tinubu Ya Naɗa Shi

Ali Nuhu Ya Karɓi Ragamar Hukumar NFC, Ya Kama Aiki Gadan-Gadan a Muƙamin da Tinubu Ya Naɗa Shi

  • Sarki Ali Nuhu ya karɓi ragamar hukumar fina-finai ta Najeriya (NFC) a hukumance a Jos, babban birnin jihar Filato
  • Hakan ya biyo bayan naɗin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya masa a matsayin manajan darakta/shugaban hukumar NFC
  • Da yake jawabi, Ali Nuhu ya ce ya shirya aiki ba kama hannun yaro domin kawo ci gaba a harkar shirin fim a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos - Shugaban huukumar fina-finai ta Najeriya (NFC), Sarki Ali Nuhu ya yi alkawarin inganta harkar fina-finai domin taimakawa tattalin arzikin kasa ya bunkasa cikin sauri.

Ali Nuhu ya yi wannan alkawarin ne a wurin bikin miƙa masa ragamar hukumar a Jos, babban birnin jihar Filato, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Ali Nuhu.
Ali Nuhu ya karbi ragamar hukumar NFC Hoto: Ali Nuhu
Asali: Facebook

Jarumin na masana'antar Kannywood ya zama shi ne manajan darakta na hukumar fina-finai ta Najeriya (NFC) na bakwai a tarihi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya kama aiki a matsayin MD na NFC, Ali Nuhu ya tabbatar wa mahalarta taron cewa ya shirya tsaf domin aiki tuƙuru da nufin inganta aikin hukumar.

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai yi amfani da dimbin kwarewarsa wajen bunkasa masana’antun fina-finai daban-daban da ake da su a Najeriya, The Sun ta rahoto.

Ali Nuhu ya kuma jaddada tsammanin da gwamnatin tarayya, masu shirya fina-finai, masu ruwa da tsaki, da al’ummar Nijeriya ke yi wa hukumar, inda ya bayyana muhimmiyar rawar da take takawa.

Wane abubuwa Ali Nuhu zai maida hankali?

MD ya ce aikin NFC ya ta’allaka ne kan lalubo hanyoyin kirkire-kirkire a Najeriya, musamman wajen shirya fina-finai, da kuma tallafa wa kokarin gwamnati na kawo ci gaban kasa.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Rundunar soji ta saduda, ta nemi agajin EFCC a wasu bangarori, ta fadi dalili

"Zan jagoranci samar da kayan aikin shirin fina-finai na zamani domin kawo ci gaba da kuma tabbatar da cewa masana'antun mu sun shiga ana gogayya da su a duniya."
“Zan daga darajar fina-finan Najeriya a gida da waje. Na shirya dabarun hadin gwiwa kamfanoni masu zaman kansu, masu ruwa da tsaki na kasa da kasa da jama'a inganta ayyukan mu."

- Ali Nuhu, shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya.

Ali Nuhu ya ziyarci Sarkin Kano

A wani rahoton kuma Shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu ya ziyarci mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero a fadarsa dake garin Kano.

Ali Nuhu ya kai wa Sarkin Kanon takardar nada shi mukami da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tare da neman tabarraki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel